ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Albishir Ga ’Yan Kasuwar Ketare Dake Kasar Sin

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Tun lokacin da kasar Sin ta sanar da inganta matakanta na yaki da annobar COVID-19, kanana da manyan harkoki na kasuwanci ke kara bunkasa a sassa daban-daban na fadin kasar. Tituna sun kara cika da ababan hawa, wuraren shakatawa da na motsa jiki ma ba a bar su a baya ba.

Ana haka ne kuma, sai hukumomi suka sanar da kaddamar da sauyi a dokar gudanar da rijistar hada-hadar cinikayyar kamfanonin ketare dake cikin kasar, duk da nufin kara bunkasa harkokin kasuwanci a kasar.

  • Jawabin Murnar Shiga Sabuwar Shekara Na Shugaban CMG 

A karkashin wannan sauyi, hukumomin da abun ya shafa, sun dakatar da neman takardun rajistar kasuwancin waje, daga kamfanonin dake hada hadar shige da ficen hajoji, da takardun shaidar rajistar fasaha ta kwangilolin shige da fice, da shaidar kayyade hajoji, da takardun shaidar gudanar da kasuwanci na gwamnati, da ma wasu sauran takardu masu nasaba da hakan. Matakin dake kara tabbatar da alkawarin kasar na kara zurfafa bude kofa.

ADVERTISEMENT

Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin a nata bangare, ta ce wannan sauyi na da matukar muhimmanci ga masu gudanar da harkokin kasuwancin waje dake kasar Sin. Kaza lika sabon salo ne da gwamnatin Sin ta bullo da shi domin bunkasa cinikayya, da sakarwa kasuwa mara.

Masu fashin baki na cewa, matakin zai taimaka wajen kyautata damar gudanar da kasuwanci a saukake, da ingiza damar bunkasa cinikayyar kamfanonin waje, da bunkasa cinikayya mai nagarta, da kara bude kofa bisa matsayin koli.

LABARAI MASU NASABA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

Wani rahoton bincike ya nuna cewa, a cikin ’yan shekarun nan, manyan kamfanonin kera kayayyaki na kasar Sin, sun samu ci gaba matuka, inda kasuwar ta kara samun darajar da ma fadada tasirinta a kasuwannin ketare.

A halin da ake yanzu, yawan kamfanonin kera kayayyaki masu hannun jari dake rukuni na A ko A-share a Turance, ya kai 2,121, wanda ya karu da kashi 69.7 bisa dari daga 1,250 a karshen shekarar 2017. Yayin da darajar manyan kamfanonin kera kayayyaki a kasuwa da aka zayyana, sun karu sosai daga shekarar 2017 zuwa ta 2021. Wadannan kamfanoni sun samu kudin shiga da yawansu ya kai yuan tiriliyan 11.79 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.69, a cikin kudaden shiga na ayyukan da suka gudana a shekarar 2021, idan aka kwatanta da yuan tiriliyan 7.47 a shekarar 2017.

Wannan na kara nuna cewa, manufar kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje na kara amsa sunanta. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow
Daga Birnin Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Kotu Ta Dakatar Da DSS Kan Cafke Shugaban Hukumar INEC

Kotu Ta Dakatar Da DSS Kan Cafke Shugaban Hukumar INEC

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.