Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi ya bayyana cewa sabon tsarin da CBN ya bullo da shi na kayyade cire kudi yana da alfanu mai yawan gaske.
Ya ce tsarin ya dade tun a 2012 lokacion da yake gwamanan babban bankin suka so bullo da shi, ya ce a yanzu CBN ya ci gaba daga inda ya tsaya.
Ya ce, “Tsarin takaita cire kudade ya samo asali ne tun a 2012 lokacin da nake gwamnan CBN, inda aka fara da Jihar Legas sannan ya watsu har zuwa jihohi guda biyar. Bayanan da muka samu a wancen lokaci, duniya tana bunkasa wanda take hana mutane rike tsabar kudi tare da samar da sabon tsarin takaita kudade wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci.
“Da farko mutane sun kalubalanci tsarin, amma daga baya sun amince da shi tare da fara yin amfani da mabanbantan tsarin biyan kudade a wuraren cin abinci da shaguna da sauran wurare,” in ji shi.
Ya kara da cewa daya daga cikin muhimmancin dokar kayyade kudade shi ne, zai hana yin magudin siyan kuri’u, sannan ya gargadi ‘yan Nijeriya su manta da ‘yan siyasan da suke korafi kan wannan doka domin su zai fi shafa sakamakon amfani da kudade da suke yi wajen sayan kuri’u.
“Ina shawartar mutane su kuda da ‘yan siyasan da suke kalubalantar tsarin dokar kayyade cire kudadde, domin su za su fi cutuwa da tsarin. Suna kwashe shekaru hudu a kan mukami ba tare da sun iya sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ba, sannan daga baya su riko makudan kudade da suke tunanin za su yi amfani da su wajen bai wa jami’an tsaro da jami’an zabe ci hanci.
“Tsarin zai kuntata wa ‘yan siyasan da ke kokarin bai wa jami’an tsaro da jami’an zabe cin hanci, dole mutum ya saka kudaden a asusunsa na kashin kai wanda kuma za a iya bincikawa. Domin haka, ina kira ga mutane su rungumi tsarin hannu bibbiyu a matsayin hanyar tsaftace dimokuradiyya da kuma hana ‘yan siyasa yin murdiya.”