Nijeriya na daga cikin kasashen da kan gaba wajen noman gyada a nahiyar Afirka, kuma ta hudu a cikin jeren kasashen dunya da ake noman gyadar.
Kasar na noma kimain tan miliyan 1.5 na gyadar a duk shekara, inda kuma ake sarrafa man da ake samu daga cikinta,don amfanin yau da kullum.
- An Yi Atisayen Karshe Na Dukkan Fannoni Don Share Fagen Karbar Kumbon Shenzhou-14
- An Shiga Firgici: ’Yan Bindiga Sun Cinna Wa Fadar Iree Wuta A Osun
Kiyasin da aka yi, shi ne, idan ka noma gyada a Nijeriya, a kadada daya, idan aka matse ta, za a iya samun mai daga gyadar gydadar da zai kai kimanin lita 500.
Ta fuskan tattalin arzikin kasa, noman na samar da ayyukan yi ga dimbin al’ummar kasa da habaka tattalin arzikin kasa.
Ana samun kudi mai yawa daga man da aka tatsa na gyada kuma sannan kuma ana samun kudaden shiga daga gyadar da aka noma. A shekarun da suka wuce, gwamnatin kasar nan, na bai wa fannin na sarrafa gyadar mahimmanci sosai.
Abubuwan Da Ake Bukata Ka Tanada Kafin Fara Tatsar Man Gyada:
Da farko dai, ana bukatar tabbatar da ka yi rijista da hukumar kula da ingancin abinci ta kasa (NAFDAC), za ka kuma dinga tuntubar kamfanin da ke cikin wannana sana’a, domin su dinga ba ka shawara.
Zuba Jari:
Bayan ka yi wa kamfanin rijista da hukumar ta (NAFDAC), hakan ya nuna a zahiri cewa, ka shirya shiga cikin aiji ke nan gadan-gadan ta hanyar zuba jarin naka. Za ka iya sayo kayan da za ka yi wannan aiki.
Mallakar Gyadar:
Abin farko da za ka fara tanada shi ne, gyadar, an fi yin nomanta, a Areawacin kasar nan da yankin Afirka maso yamma.
A Nijeiya, jihohin da aka fi yin noman gyada sun hada da,Kano da Kaduna da Taraba da Bauchi da Borno da Adamawa, inda wadannan jihohin, ke noman da yawan ta ya kai kimanin kashi 83 a cikin dari zuwa kashi 88.
Kayan Da Aka Fi Aikin Da Su: Kayan da ake fi yin aikin na tatsar man gyadan sun hada da, injin yin aikin.
Jarin Da Za Ka Zuba A Fannin: Ga wanda yake karamin dan kasuwa zai iya fara wa da kimanin naira miliyan 10.5 zuwa naira miliyan 15, amma ga wanda yake yana da kudi da yawa don shiga fannin, zai iya fara wa da naira miliyan 25 zuwa naira miliayan 65.
Yawan Ribar Da Ake Samu A Fannin: Ga wanda yake karami a fannin, zai iya samun ribar da ta kai ta naira miliyan 15 zuwa naira miliyan 22; inda kuma wanda shi mai karfi ne a fannin, zai iya samun kudaden shiga da su kai kimanin daga naira miliyan 35 zuwa naora miliyan 70.