Shugaban Masu Rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya karyata labarin cewa ya yi barazanar fallasa gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje kan zargin cire wa ma’aikatan kananan hukumomin jihar daga albashi.
Doguwa, mai wakiltar mazabar Doguwa-Tudun Wada a Jihar Kano kuma shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, ya bayyana labarin a matsayin mugun nufi da kokarin bata masa suna.
- Kwastam Ta Kama Kayan Fasa Kwauri Da Kudinsu Ya Kai Miliyan 78.6 A Kebbi
- Yunkurin Wasu Tsirarun Kasashe Na Bata Sunan Kasar Sin Ta Fakewa Da Kare Hakkin Bil Adama Ya Sake Cin Tura
Da yake mayar da martani kan rahoton da wata kafar yanar gizo ta wallafa, Doguwa ya karyata rahoton sannan ya ce babu wata matsala tsakaninsa da gwamnan jihar.
Dan majalisar ya bukaci kafar da ta wallafa labarin sa’o’i 48 don su cire tare da neman afuwarsa.
“Gwamnanmj ya kasance uba a gare ni, shugabana kuma mai ba ni shawara har abada, duk da labaran karyar da yada don hada mu husuma.”