Muhammad Adamu Aliero ya kayar da Gwamnan Jihar Kebbi a takarar kujerar Sanatan Kebbi ta Tsakiya, inda ya samu kuri’u 126,588 yayin da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya samu kuri’u 92,389.
A lokacin da ya ke bayyana sakamakon zaben, Sanatan mazabar Kebbi ta Tsakiya, Farfesa Abbas Yusuf Bazata, ya ce “Sakamakon zaben kujerar Sanatan mazabar ta Kebbi ta Tsakiya da aka gudanar a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu ya bayyana kamar haka Sanata Muhammad Mainasara Adamu Aliero ya lashe zabe da kuri’u 126,588 da aka kada kuma suka lashe mafi yawan kuri’u, an bayyana su a matsayin wanda ya lashe zaben,” in ji shi.
- INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Sanatan Zamfara Ta Tsakiya Bai Kammala Ba
- Tinubu Ya Yi Nasara A Jihar Zamfara, Ya Kayar Da Atiku, Kwankwaso Da Obi
Haka kuma Abubakar Atiku Bagudu ya samu kuri’u 92,389 a zaben da aka gudanar.
Ya bayyana cewa sauran ‘yan takarar jam’iyyun siyasa sun samu kuri’u daban-daban kamar yadda aka bayyana.
“Ya ce a matsayina na jami’in zabe da kuma karba da tattara sakamakon zaben kujerar Sanatan majalisar dattawa na Kebbi ta Tsakiya, kuma ikon da ya rataya a wuyana.
“Na ayyana Sanata Muhammad Mainasara Adamu Aliero na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben kuma ya samu mafi yawan kuri’un da aka kada kuma shi ne zababben Sanata na Mazabar Kebbi ta tsakiya a majalisar dattawa.