Alkaluman hidimar cinikayya ta yanar gizo na Sin, wanda ke auna yanayin ayyukan samar da hidimar sayayya da aikewa da kayayyaki ta yanar gizo a kasar, sun kai maki 110.9 a watan Yulin da ya gabata, adadin da ya karu da maki 0.3 idan an kwatanta da na watan Yuni.
Hukumar dake lura da sashen samar da hidimar aikewa da sakwanni da sayayya ta kasar ce ta fitar da alkaluman, wadanda suka kunshi musamman mizanin gamsuwar al’umma a fannin, wanda ya kai maki 101.2 a watan na Yuli, adadin da ya karu da maki 1.5 idan an kwatanta da na watan Yuni, yayin da fannin samun bayanai kai tsaye daga hajojin sayayya ke ci gaba da bunkasa cikin watanni 7 a jere, har zuwa wata na Yuli, adadin da ya karu da maki 0.3 idan an kwatanta da na watan Yuni.
Har ila yau, alkaluman fannin bin bahasin adadin kayayyakin da aka saya ta yanar gizo a watan na Yuli sun karu zuwa maki 121.8, wanda ya shaida raguwa kadan, ta maki 0.8 kan na watan Yuni. Wannan raguwa da aka samu a watan Yuli, ta faru ne sakamakon karewar hada-hadar tallace tallacen hajoji masu rangwame a watan Yuni.
An tattara alkaluman hidimar cinikayyar ta yanar gizo na kasar Sin ne daga bayanan da kamfanin sayayya ta yanar gizo na JD.com ya samar, kamfanin da shi ne kan gaba a fannin a duk kasar Sin. An kuma sanya maki 100 a matsayin mafi karancin maki na alkaluman da za a tattara. (Saminu Alhassan)