• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Alkawarin Da Tinubu Ya Yi Wa Ma’aikatan Gwamnati

by Yusuf Shuaibu
3 years ago
Tinubu

Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ma’aikata tabba-cin samun kyakykyawan rayuwa a gwamnatinsa.

Ya ce zai ba su fiye da mafi karancin albashi da za su iya gudanar da rayuwarsu da ta iyalansu.

  • Na Gwammace Zama Mashawarci A Gefe, Ba Shugaban Ma’aikatan Tinubu Ba – El-Rufai

Ya kuma yi alkawarin zama amintaccen aminin ma’aikatan kasar nan da zaran an rantsar da gwamnatinsa a ranar 29 ga Mayun 2023.

Wadannan alkawuran na kunshe ne a cikin sakon bikin ranar ma’aikata na wan-nan shikerar da ya sanya wa hannu.

Da yake tabbatar wa ma’aikatan kasar nan ta hannun kungiyar kwadago (NLC) da kuma kungiyar ‘yan kasuwa (TUC), Tinubu cewa “Da zarar an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu a matsayin shugaban Nijeriya, ma’aikata za su samu fiye da mafi karancin albashi. Za ku sami albashi fiye da mafi karancin albashi da za ku iya gudanar da rayuwarku da ta iyalanku.

LABARAI MASU NASABA

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

“A karkashin shugabancina, za ku sami ‘yanci da walwalan aiki wajen yakir rashin adalci na zamantakewa da tattalin arziki ga daukacin ‘yan Nijeriya, gami da duk ma’aikata.

“Yakinku zai zama yakina, saboda a ko da yaushe ni zan muku yaki. Ina da shirye-shiryen inganta walwala da yanayin aiki mai kyau a cikin ajandar gwamnatina, saboda samar da ingantaccen Nijeriya.

Alkawari ne akai na tun lokacin da aka hai-fe nake kokarin yadda za a inganta rayuwar ma’aikata.”

Da yake kiran hadin kan ma’aikata, Tinubu ya shawarce su da cewa, “Kwanaki masu zuwa, ana bukatar fahimtar juna da hadin kai daga kowane bangare, saboda shugabanci na bukaci mu dauki tsauraren matakai domin jama’armu da ma’aikatan Nijeriya su samu rayuwa mai inganci.”

Zababben shugaban kasar ya nemi goyon daukacin ma’aikatan Nijeriya, inda ya nemi ma’aikata da su hada kai da gwamnatinsa mai jiran gado wajen yakir fatara, jahilci, cututtuka, rashin hadin kai, kabilanci da mambancin addini da duk wani mummunan lamari da ka iya barazana ga zaman lafiya da hadin kan kasa.

Tinubu ya yaba da irin rawar da ma’aikatan Nijeriya suke takawa wajen gina kasa.
Ya ce, “Na bi sahun sauran kasashen duniya da sauran ‘yan’uwa domin murnar ranar ma’aikata ta duniya ta bana. Yau rana ce ta musamman a mafi yawan kasashen duniya, rana ce ta gaisuwa da karrama ma’aikatan da kwazonsu da guminsu ke ci gaba da rura wutar ci gaban Bil’adama.

“Wannan rana tana da matukar mahimmanci ta fuskoki da yawa. Rana ce da aka kirkira saboda gwagwarmayar neman hakkin ma’aikata da ‘yancinsu na zaman-takewa da tattalin arziki. Tun daga shekara ta 1891, aka fara bikin wannan rana a duk fadin duniya.

“A Nijeriya, kowace ranar 1 ga Mayu rana ce ta musamman a kalandar kasarmu. Ranar hutu ce ga al’umma da muke yi ba wai don tunawa da gudunmawa da sa-daukarwar da ma’aikata suke bayarwa ba ne don ci gaban kasarmu ce.

Ta kasance ranar bikin hakkin ma’aikata da kare mutuncisu da ingantaccen albashi da rayuwa mai kyau, kuma mafi mahimmanci shi ne, muhimmiyar rawar da kungiyar kwadago ke takawa wajen hadin kan kasarmu.

“Tun a shekarar 1945 lokacin da ma’aikatan jirgin kasa da wasu kungiyoyin ma’aikatan gwamnati 16 suka jagoranci yajin aikin farko na neman karin albashi sakamakon tsadar rayuwa, kungiyar kwadago a Nijeriya a ko da yaushe tana yaki domin talakawan kasarmu.

Ba abin mamaki ba ne cewa kungiyar ta kara kuzari ga gwagwarmayar neman ‘yancin kai ta hanyar hada kai da masu kishin kasa irin su Nnamdi Azikiwe, Herbert Macaulay, Ahmadu Bello, Obafemi Awolowo, Ernest Ikoli da Anthony Enahoro da sauransu.

“Haka kuma an samu kungiyar kwadago a Nijeriya ne a daidai lokacin da muke gwagwarmayar maido da mulkin dimokuradiyya. Kungiyar kwadago ta Nijeriya da kungiyoyin da ke da alaka da ita kamar irin su NUPENG, Tedtile, PENGASSAN, da dai sauransu, sun hada kai da shugabanni da kungiyoyi masu fafutukar tabba-tar da dimokuradiyya wajen maido da mulkin dimokuradiyya a Nijeriya a shekarar 1999 bayan kusan shekaru biyu na mulkin kama-karya na sojoji.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya
Tambarin Dimokuradiyya

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

November 7, 2025
Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta
Tambarin Dimokuradiyya

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
Next Post
‘Yansanda Sun Damke Wani Mutum Da Ya Kashe Matarsa A Adamawa

'Yansanda Sun Damke Wani Mutum Da Ya Kashe Matarsa A Adamawa

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno

November 10, 2025
Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.