Allah ya yi wa babban limamin masallacin Juma’a na cikin garin Garun Kura, Sheikh Imam Gwani Alaramma Ali Dan’a Lungun Liman, da ke karamar hukumar Kura a jihar Kano rasuwa.
Wata majiya da ke da kusanci da limamin ce ta shaida mana rasuwa shehun malamin.
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sace Buhari Da El-RufaiÂ
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Kansila A Adamawa
Ya rasu da sanyin safiyar ranar Lahadi, kuma za a yi jana’izzarsa da misalin karfe 2 na rana.
Tuni shugaban karamar hukumar Kura, Mustafa Abdullahi Rabiu da Dokajin Rano, Hakimin Kura, Abubakar Tijjani Abubakar suka yi alhinin rasuwar babban limamin.
‘Yan uwa da abokan arziki da almajiran shehun malamin suka shiga jimamin rashinsa, inda kowa ke masa fatan samun rahama da rabautat Ubangiji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp