Mawaki kuma mai shirya fina-finai a masana’antar Kannywood, Mu’azu Muhammad Birniwa wanda aka fi sani da El-Mu’az Birniwa ya rasu a wani yanayi mai cike da tsoratarwa.
Rahotanni sun tabbatar da cewar a daren ranar Laraba El-Mu’az na daga cikin ‘yan uwa da abokan arziki da suka buga kwallon kafa domin taya mawaki Auta Waziri murnar auren da zai yi.
- Akwai Bukatar Mu Bai Wa Mbappe Lokaci Domin Dawowa Kan Ganiyarsa – Ancelotti
- Google, Microsoft, TikTok Sun Biya Gwamnatin Nijeriya Harajin N2.55trn A 2024 – NITDA
Amma a lokacin buga wasan marigayin ya bayyana cewar yana ganin jiri hakan ya sa ya fita daga filin wasan.
Fitarsa daga wajen ya nufi wani asibiti da ke kan titin Waff road, a Jihar Kaduna inda a nan ne rai yayi halinsa.
Kafin rasuwar El Mu’az ya shaharaa a fagen wakokin fadakarwa da soyayya.
An haifi Mu’azu Muhammad Birniwa a garin Kaduna, amma asalinsa dan garin Birniwa ne da ke Jihar Jigawa.