Al’ummar Arewa Za Su Fi Kowa Cin Gajiyar Gwamnati Da Majalisar Dinkin Duniya

NEW YORK, NY - SEPTEMBER 19: President Donald Trump speaks to world leaders at the 72nd United Nations (UN) General Assembly at UN headquarters in New York on September 19, 2017 in New York City. This is Trump's first appearance at the General Assembly where he addressed threats from Iran and North Korea among other global concerns. (Photo by Spencer Platt/Getty Images)

Da yake jawabi a madadin wakilin Gwamnatin Tarayya, Mista Suffyan Koroma ya ce; wannan ayyukan da aka gudanar tsakanin Gwamnatin tarayya da Majalisar Dinkin Duniya, da ma abu ne da ya dace ace al’umman karkara sun amfana da shi, kuma yana cikin kudurorin Gwamnatin Tarayya, sai ga shi ta samu hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya.
Ya kara da cewa; baya ga wannan aikin na samar da ruwan sha mai inganci, akwai ayyuka da dama da ake kokarin samarwa wanda za a koyar da al’umman da ke rayuwa cikin kunci a wadannan yankunan.
Hukumar kula da harkokin ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya, ta samar da abubuwan ci gaba mai yawa a Arewacin Nijeriya. Cikin kudurorin Majalisar Dinkin Duniya guda goma sha bakwai, akwai wadanda suka samu gudana a Arewacin Nijeriya.
Hukumar ci gaban baidaya na Majalisar ta fara magance matsalar talauci da ke addabar mafiya yawan al’umman Arewa da ke zama a karkara da wadanda rigingimun Boko Haram da ma na kabilanci ya addaba. Ta hanyar koyar da su kananan sana’o’i da za su dogara da kawunansu.
Haka-zalika, akwai batun kawar da yunwa musamman ga al’umman da ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira.
Samar da ruwan sha mai inganci, wanda zai taimaka wa al’umma mazauna karkara da ma mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira. Da tsaftace gurare musamman inda jama’a ke rayuwa. Tsaftataccen ruwan sha zai taimakawa al’umma wajen samun lafiya da kyakkyawar rayuwa.
Samar da abinci mai inganci na gina jiki da koyar da harkokin Noma musamman ga wadanda ke rayuwa cikin kunci.
Shirin samar da ruwansha mai tsafta wanda majalisar Dinkin Duniya ta samu hadin gwiwa da Gwamnatin tarayya ya amfani al’umman karkara da ke zama a Arewa maso gabashin Nijeriya.
An gudanar da gina rijiyoyin burtsatse guda goma –goma a kauyuka da ke Arewa maso gabashin Nijeriya da yawansu ya kai 460.

Exit mobile version