Connect with us

LABARAI

Al’ummar Gawassu Sun Nemi Gwamnatin Kebbi Ta Kawo Musu Dauki

Published

on

A Jiya ne jama’ar garin Gawassu da ke a cikin karamar hukumar mulki ta Birnin-kebbi sun koka kan Lalacewar Asibitin garin da kuma rashin kyakyawar hanyar shiga garin ne Gawassu a lokacin damana. Inda jama’ar garin suka nuna cewa a duk lokacin da ake ruwan sama sukan faskanci barazanar rashin hanyar shiga garin da kuma fitowa wanda dole ne jama’ar garin ko kuma baki su yi iyo cikin ruwan da ke kwantawa a hanyar shiga gari da kuma fitowa.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban mazabar ta Gawassu na jam’iyyar APC  Alhaji Aliyu Abdullahi Gawassu da yake magana a madadin jama’ar yankin ta Gawassu da kewayen ta ga mai neman takarar kujerar dan majalisar wakilai na mazabun Birnin-Kebbi, Kalgo da Bunza a majalisar dokoki ta tarayya, Alhaji Abu Najakku wanda ake kira da suna dan Bello yayin da ya kai ziyara a garin na Gawassu domin neman goyon bayan shuwagabannin mazabar ta Gawassu a jiya tare da tawagarsa.

Haka kuma shugaban mazabar ya cigaba da bayyanawa mai neman takarar kujerar dan majalisar wakilai Abu Najakku  irin matsalolin da kuma damuwar su a lokacin  damana da kuma irin halin ko in kula da gwamnatin tayiwa  Asibitin garin na Gawassu wanda a halin yanzu mata da maza marasa Lafiya  na yankin garin na shan wahalar gaske wurin  samar da kiyon Lafiya ga jama’ar  yanki. Kazalika yace “ idon mace ko namiji bayada Lafiya sai an dauke shin zuwa Asibitin garin Birnin-kebbi wanda kafin akai mara lafiya zuwa Asibitin  Birnin-kebbi zai shiga cikin babbar damuwa saboda wuri ba kusa bane”.

Da yake jawabi ga shuwagabanin mazabar Gawassu Alhaji Abu Najakku ya bayyana rahin jindadinsa ga irin halin da jamar’ar garin Gawassu suke cikin musamman rashin kyakyawar hanya ta shiga garin na Gawassu da kuma irin yadda Asibitin ta lalace , saboda haka nuna tausayawar sag a jama’ar garin inda yace” zan yi iya kokarina na ganin cewa na isar da koken ku ga gwamnatin da kuma hukumomin da abin ya shafa domin kawo muku dauke”. Ya kuma yi amfani da ziyarar domin basu hakuri da cewa “ gwamnatin Sanata Abubakar Atiku Bagudu na iya kokarin ta na ganin cewa ta bunkasa kiyon Lafiya da kuma hanyoyin mota ga jama’ar ta , saboda haka kuma kara hukuri nan bada jimawa ban a tabbatar Gwamna Bagudu zaya magance wannan matsala da kuke faskan ta”. Daga nan yayi kira ga jama’ar yanki das u cigaba da baiwa gwamnatin Bagudu da kuma shugaba Muhammadu Buhari goyon bayan da kuma zaben sa a matsayin dan majalisar wakilai na mazabun Birnin-kebbi, Kalgo da Bunza a majalisar dokoki ta tarayya domin In zama wakilin ku
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: