Mazauna garin Durbi Takusheri da ke karamar hukumar Mani a jihar Katsina sun bukaci gwamnati da ta magance taɓarɓarewar hanyoyinsu da kuma matsalar karancin ruwan sha da ke addabar al’ummarsu.
Wani mazaunin garin, Murtala Yusuf wanda ya yi magana a madadin shugaban al’ummar ya bukaci Gwamna Dikko Umar Radda da ya cika alkawarin da ya dauka na gyara hanyar da ta bi zuwa yankinsu.
“Mun yaba da jajircewar gwamnan, amma muna rokonsa da ya gyara mana hanyarmu kamar yadda ya tabbatar mana,” in ji Yusuf.
Ya kuma bayyana kalubalen samar da ruwan sha da al’umma ke fuskanta, inda ya bayyana cewa suna da rijiyoyin burtsatse, amma ba sa aiki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp