Al’ummar Yamaltu Sun Samu Tallafin Bunkasa Ilimi Daga Dan Majalisarsu

Daga Bello Hamza Abuja,

Kamar yadda aka san Hon. Yunusa Abubakar Ustaz mai wakiltar mazabar Yamultu a majalisar tarayya, yana gaba gaba idan ana maganar kawo cigaba a mazabarsa, musamman ta bangaren ilimi, a wannan karon ma dan majalisar ne ya dauki nauyin horas da Malamai domin sanin makamar aiki inda aka dauko kwararru daga Cibiyar Horas da Malamai ta Tarayya (National Teachers Institute Kaduna) domin bayar da wannan horaswar. Mun samu zantawa da Ahmed Gambo Mu’azu daya daga cikin masu bayar da wannan horo kuma ya ce, wannan ya yi daidai a tsakanin takwarorin sa ‘yan sisyasa wajen yin taruka na kara wa juna sani da kuma horas wa ga su malamai domin samun kyakkyawar yanayi na bunkasa fannin ilimi.

Muhammad Gambo Mu’azu ya fara da mika godiya ga Allah da kuma shi dan majalisa da ya dauki nauyin gudanar da wannan ‘Workshop’ na horas da malamai, yana mai yabawa dukkan wadanda suka bayar da gudumawar ganin shirin ya samu nasara, y ace, horaswar zai matukar taimaawa Malamai musammman na matakin Firamari. Ya ce, dole a yaba wa dan majalisar musamman ganin shi ne ya sanya kudinsa da lokacinsa na ganin an samu nasarar taron horaswar.

Ya kuma yi kira ga malaman da suka samu halartar taron su yi kokari su tabbatar cewa sun yi amfani da wannan dama da aka basu su fahimci abin da aka koya masu kuma tabbatar cewa sun koma sun taimaka wa musamman sauron malaman da ba su zo nan ba.

A nasa jawabin, wakilin dan majalisar (Hon. Yunasa Abubakar Ustaz), Abu Ali Dan Rimin Yamaltu, ya bayyana cewa, Hon Yunasa Abubakar Ustaz baya wasa a bangaren samar da ingantaccen ilimi ga al’umma. Ya kuma ce, a nan gaba za a sake gudanar da irin wannan horaswar don wadanda basu samu zuwa a wannan karon.

Exit mobile version