Connect with us

LABARAI

Al’ummar Zuru Mazauna Kaduna Sun Raba Tallafin Kayan Abinci Ga Marayu

Published

on

Kungiyar Al’ummar Zuru Mazauna Jihar Kaduna karkashin jagorancin Wakilin Zurun Kaduna, Injiya Zubair Kabiru, sun raba kayan tallafin abinci ga Mata da kuma Kananan Yara Marayu na Al’ummar Zuru Mazauna Jihar Kaduna dake daukacin Kananan Hukumomi 23 dake fadin Jihar Kaduna.

A nasa jawabin, wakilin Al’ummar Zurun mazauna Jihar Kaduna, ya bayyana cewa, wannan masarauta tayi tunanin irin halin matsin rayuwar da ake ciki, musamman a daidai irin wannan lokaci da Al’umma ke cikin kuncin halin rayuwa, musamman Mata da yara Marayu da suka rasa Iyayensu.

Wakilin Al’ummar Zurun mazauna Jihar Kaduna, ya kara da bayyana cewa, a karo na farko sun fara da raba kayan abinci ga Marayu a kalla su 800 a karo na farko, wanda kuma suna sa ran nan da dan wani lokaci za su ci gaba da gudanar da hakan idan.

Injiya Zubair Kabir, ya kuma bayyana godiyarsa ga Uba a gare su, Maimartaba Sarkin Zuru, Janar Sani Same, bisa yadda ko da yaushe kofarsa a abude take wajen irin gudunmuwar da yake baiwa Al’ummar Zuru dake fadin kasar nan baki daya. Sannan ya kuma mika godiyarsa ga Maimartaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris, a bisa irin gudunmuwar da yake baiwa Al’ummar Zuru Mazauna Jihar Kaduna, wanda a cewarsa, suna mika godiyarsu da kuma jinjina ga Maimartaba Sarkin Zazzau da kuma Masarautar Zazzau baki daya.

Wakilin Zurun Kaduna, ya kuma mika godiyarsu ga wadanda suka bayar da gudunmuwar kudi da kayan abinci, domin ganin an tallafawa wadannan Marayu, musamman Major Janar AB Ibrahim, wanda shi ne ya dauki nauyin kashi hamsi na tallafin kayan abincin da aka raba. Sannan ya kuma mika godiyarsa ga Birgediya Janar Musa Ibrahim, da kuma Shugaban kamfanin Maryam Pharmacy dake Unguwar Dosa, da sauran daukacin Mutanen da suka bayar da nasu tallafi.

Daga karshe ya kuma mika godiyarsa ga ‘yan kwamitin Marayu, karkashin jagorancin Babban Limamin Masallacin Choice Plaza dake Alkali rod a Kaduna, Sheikh Ibrahim Rafin Gamo, a bisa irin Namijin kokarin da suka nuna wajen sauke nauyin da aka daura masu.

A yayin da take mika na ta godiyar, a madadin wanda suka amfana da tallafin Maryam magaji Abakwa, ta bayyana farin cikinsu da irin wannan gudunmuwan tallafin kayan abinci da wannan Kungiya ta Al’ummar Zuru Mazauna Jihar Kaduna suka basu. A cewarta.
Advertisement

labarai