Al’ummun Pakistan Suna Cike Da Imani Kan Rigakafin Sin

Daga CRI Hausa

A ranar 8 ga wata, ministan kula da shirin raya kasa da ayyukan musamman na kasar Pakistan Asad Umar ya bayyana cewa, kawo yanzu gaba daya adadin al’ummun kasar wadanda aka yi musu allurar rigakafin cutar COVID-19 a kamfanoni masu zaman kansu ya kai dubu 14, kuma adadin al’ummun kasar da suka karbi allurar a hukumomin gwamnati ya kai miliyan 1.1, wato kowace rana adadin yana kai sama da dubu 76, ministan ya kara da cewa, an samu yawancin allurar ne daga kasar Sin.
Mazaunin birnin Islamabad, Baqir Ali, ya nuna godiya ga kasar Sin saboda ta samarwa kasarsa tallafin allurar, inda ya bayyana cewa, “Mun godewa allurar rigakafin kasar Sin matuka, al’ummomin kasashen Sin da Pakistan dadaddun abokai ne, yanzu haka kasar Sin tana samarwa Pakistan allurar, ana sa ran za a shawo kan yaduwar annobar a kasarmu tun da wur wuri.”
Mai aikin jinya Shazil Nawaz, shi ma ya gayawa manema labarai cewa, ya yi amanna cewa, za a kawo karshen annobar COVID-19 a Pakistan a kan lokaci sakamakon yin allurar a fadin kasar.
Tun daga ranar 1 ga watan Fabrairun bana, gwamnatin kasar Sin ta riga ta samar wa Pakistan allurar rigakafin Sinopharm har sau biyu, rundunar sojojin ‘yantar da al’ummun kasar Sin ita ma ta ba da tallafin allurar rigakafin kamfanin Sinopharm ga rundunar sojojin kasar ta Pakistan, kuma tun daga ranar 3 ga watan Fabrairun da ya gabata, an kaddamar da aikin yin allurar rigakafin kasar Sin a fadin kasar, daga masu aikin kiwon lafiya da tsoffi.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version