Connect with us

RAHOTANNI

Ambaliya A Kebbi: Sanata Yahaya Ya Bada Tallafin Naira Miliyan Daya

Published

on

A jiya ne aka tabka ruwan sama kamar da bakin kwarya a garin Dakingari a karkashin karamar hukumar mulki ta Suru a jihar Kebbi, inda sakamakon tabka ruwan saman suka lalata gidaje da kuma sauran wasu dukiyoyin Miliyoyin Nairori a garin .

Bisa ga hakan ne Sanata Mai wakiltar mazabar Kebbi ta Arewa a majalisar dattijai  wato ( Kebbi North Senatorial District) daga jihar kebbi ,  Sanata Yahaya Abdullahi wanda  a halin yanzu shi ne ke rike da mukamin shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai da ke a Abuja wato (majority Leader)  ya samu labarin irin barnar ruwan da aka samu a garin Dakingari da ke daya daga cikin inda ya ke wakilta a majalisar  dattijai ta Tarayya, inda  gidaje da kuma dukiyoyin Miliyoyin Nairori barnar ruwa ta lakume inda ya aiko tawaga zuwa garin na Dakingari domin yi musu jaje da kuma basu tallafi na Naira Miliyan Daya domin rage musu asarar da suka tabka sakamakon barnar ruwan da suka samu a jiya.

Tawagar ta samu jagorancin Mataimakin shugaban karamar hukumar mulki ta Argungu, Alhaji DanLarba Tela tare da sauransu da ke rako shi zuwa fadar Lamidon Dakingari, Alhaji Jafaru Haliru amada din  Sanata Yahaya Abdullahi don jajenta wa mutanen da lamarin ya shafa da kuma masarautar da garin na Dakingari.

Inda shugaban tawagar Alhaji DanLarba Tela ya jajenta wa mutanen da kuma Lamidon Dakingari inda ya bada tallafin Naira Miliyan Daya gudumawar da sanatan ya bayar ga mutanen ganin irin barnar da ruwan sama suka yi wa mutanen garin Dakingari a jiya.

Haka kuma Shugaban ya roki Allah da ya maida musu da alhairi ya kuma kiyaye gaba, ya kuma tabbatar wa da masarautar da mutanen cewa” Sanata Yahaya Abdullahi zai yi iya kokarin sa na ganin cewar ya gabatar da koken su ga hukumar NEMA domin basu agaji na gaggawa kan irin a sarar da suka yi kan barnar ruwan da ya samu, inji shi”.

Bugu da kari ya kara da basu hakuri da kuma basu shawara na su barwa Allah al’amarin sa.

Shi ma a nashi jawabi Lamidon Dakingari, Alhaji Jafaru Haliru ya godewa Sanatan kan irin namijin kokarin da yake yi a duk lakacin da wani abu maikama da irin wannan ya samu a wannan masarauta da kuma irin wakilci mai inganci da yake yiwa mutanen mazabar Kebbi ta Arewa a majalisar dattijai ta Tarayya da ke a Abuja . Saboda amada din jama’ar garin Dakingari da kewaye muna mika godiyar mu ga maigirma Sanata Yahaya Abdullahi kan kokarin sa ga mutanen mazabar sa.

Ya kuma kara da cewar ” jama’ar garin Dakingari da keyawa na tare da sanata, zasu kuma ci gaba da bashi goyon baya domin ya kara samun kwarin gwiwar yiwa mutanen mazabar Kebbi ta Arewa wakilci mai inganci, inji Lamido”.

Daga karshe ya yaba wa sanatan da kuma sauran mutanen da ke bai wa sanatan shawara kan wakilci ta yake yiwa jama’ar mazabar Kebbi ta Arewa a majalisar dattijai.
Advertisement

labarai