Sama da fursunoni 200 ne suka tsere daga gidan yarin birnin Maiduguri da ke Jiha Borno, sakamakon ambaliyar ruwa ta rusa katangar gidan yarin.
Daya daga cikin jami’an da ke tsaron gidan yarin da ya bukaci a sakaya sunansa, ne ya tabbatar wa da RFI cewa, fursunonin sun yi amfani da damar Iftila’in ambaliyar wajen tserewa.
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ya Shaida Cewa Ba Lallai Ba Ne A Ci Nasara Daga Faduwar Wani Bangare Ba
- Kasar Sin Mai Fada Da Cikawa
Kazalika, jami’in ya bayyana cewa, akwai mayakan Boko Haram a cikin fursunonin da suka tsere.
A bangare guda, akwai wasu fursunoni sama da 200 na daban da su kuma aka sauya musu gidan yari kamar yadda jami’in ya yi karin haske.
Ambaliyar ta kuma rusa dakunan jami’an da ke tsaron gidan yarin.
Wannan na zuwa ne a yayin da al’ummar jihar ke cikin zulumi biyo bayan ambaliyar ruwan da ta mamaye yankuna da dama a cikin tsakar dare.
Sai dai hukumar bayar da agaji ta jihar (SEMA), ta ce lamarin ya munana fiye da yadda ake zato, amma ta ce tana iya bakin kokarinta na ganin an ceto wadanda lamarin ya shafa.