A yayin da manoma a fadin wannan kasa ke shirye-shiryen fara noman bana, wasu yankuna a Jihar Neja ba za su samu damar yin noman banan ba.
Wannan lamari, ya faru ne, sakamakon ambaliyar ruwan sama da ta lalata gonakin nasu.
- Gwamna Uba Sani Ya Nada Bashir Zuntu A Matsayin Babban Akanta Na Jihar Kaduna
- Kotu Ta Daure Wasu Mutum Biyu Da Suka Yi Wa Yarinya ‘Yar Shekara 14 Fyade A Birnin Kebbi
Yankunan da lamarin ya shafa, sun hada da Muye, Apataku, Egba, Ebwa, Bina, Achiba, Dere, Cheku, Sokun da kuma Arah.
Kazalika, akwai kuma matsalar ambaliyar ruwa daga Kogin Gurara, wanda hakan ya tilasta manoman barin gonakinsu da kuma sana’ar kamun Kifi.
Gonakin, wadanda da damansu a baya suka yi fice wajen noman amfani Rogo, Masara, Shinkafa da sauran makamantansu, yanzu manoman sun yi watsi da su.
Wasu daga cikin manoman a wadanan yankuna sun bayyana cewa, sun koma neman wasu gonakin da za su yi shuka ko dai a cikin jihar ko kuma a wasu guraren daban, musamman duba da cewa; sun dogara ne a kan wadannan sana’o’i na noma da kamun Kifi.
Koda-yake dai, gwamnatin tarayya ta yi wani gini mai tsawon zurfin kimanin mita bakwai da nufin dakile ambaliyar ruwan daga Kogi, amma tuni ginin ya rushe tun daga farkon aikin.
An dai gaza sake yin aikin ginin, yau kusan shekara uku zuwa hudu.
Bugu da kari, tuni wasu gonaki, musamman a yankin na Muye da ake da kadada 2.6, aikin yin noma ya tsaya cak, inda kuma mazauna yankin a halin yanzu ke zuwa wasu guraren, domin hada-hadar saye da sayarwar amfanin gona.
Wani mazaunin yankin, Ebwa Ibrahim Saidu ya sanar da cewa; akwai bukatar samar da daukin gaggawa a kan wannan matsala.
“Wasu manoma a yankin, sun koma wasu yankunan, domin neman gonakin da za su yi noma, domin ba za iya sake yin wani noma a gonakin nasu ba, sakamakon faruwar wannan matsala,” in ji Ibrahim.
Ya ce, akasarin matasanmu yanzu, sun koma Jihar Kogi don yin harkar Achaba.
Shi ma Dagacin Muye, Alhaji Salihu Muhammad ya tabbatar da wannan matsala.
“An yi aikin sake gina madatsar ruwar ne, tun bayan shekara uku zuwa hudu da suka gabata, wacce kuma ta sake rushewa a lokacin kakar noman bara, wanda hakan ya jawo lalata gonakinmu da dama“.
“Gwamnatocin baya, sun yi kokrin sake gina madatsar ruwan, amma idan Kogin ya yi ambaliya, sai ta sake lalacewa“ in ji Salihu.
Kazalika, Mukaddashin Manajan Darakta na Riko a Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Kasa (N-HYPPADEC), Mista Jimoh Haruna Gabi, a lokacin kaddamar da sake aikin ginin madatsar ruwan ya sanar da cewa, aikin zai lakume sama da Naira miliyan 600.
Ya kara da cewa, hukumar ta sake gyara kadadar noma 2.6, domin manona su sake komawa gonakinsu, don fara nomansu.
A cewarsa, sake aikin na madatsar ruwan, ana sa ran kammalawa a watan Yuli, kafin ruwan sama ya fara sauka a watan Agusta.
Shi ma, dan Majalisa mai wakiltar mazabar Agaie/Lapai ta tarayya Abdullahi Mahmud, ya bukaci a samar wa da manoman wadannan yankunan dauki, musamman duba da cewa; sana’ar noma ce akasarin al’ummar wadannan yankuna, suka mayar da hankali a kai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp