Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar Adamawa ya karu zuwa 23.
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan waɗanda suka rasu a ibtila’in da ya auku a ranar Lahadi.
- Sojoji Sun Cafke Wani Soja Kan Mutuwar Mai Gyaran Waya A Adamawa
- Adamawa Ta Amince Da Mafi Ƙarancin Albashi Na ₦70,000 Ga Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi
Gwamnan ya nuna damuwarsa da alhini matuƙa bayan ganawa da waɗanda ambaliyar ta rutsa da su, yana mai cewa irin wannan al’amari mai muni bai taɓa faruwa ba a baya ba.
Ambaliyar ta faru ne da misalin ƙarfe 1 na safiyar Lahadi a sakamakon ruwan sama mai yawa da aka yi, wanda ya haddasa mutuwar mutane 23 da kuma lalata dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira.
Yayin jawabi ga waɗanda abin ya shafa a sansanin wucin gadi da aka kafa a Kwalejin Aliyu Mustafa, Yola, Gwamna Fintiri ya sanar da kafa kwamitin na musamman don tantance adadin asarar da aka yi.
Ya bayyana halin da aka shiga mara daɗi, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka yi asarar dukiyoyi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta tallafa musu wajen sake gina musu gidajen su da sauya muhallinsu.
Fintiri ya kuma soki waɗanda ke yaɗa rahotannin ƙaryar game da lamarin, ba tare da fahimtar ainihin abin da ke faruwa ba, inda ya ce hakan yana da nasaba da tuggun siyasa da son zuciya.
Ya bayyana cewa maƙasudin ambaliyar sun haɗa da ruwan sama mai yawa da toshewar hanyoyin ruwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp