Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kafa wani kwamiti da zai gaggauta yin nazari da magance yawan ambaliyar ruwa da ake samu a fadin jihar.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne, ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar a jiya Litinin a Kano.
- Za A Sake Jera Kwana Hudu Ana Zabga Ruwan Sama A Jihohin Arewa Biyar – NiMet
- Ɓarnar Ambaliyar Ruwa A Jigawa
Ya ce gwamnatin jihar ta damu matuka da irin ambaliyar ruwan da ke faruwa a jihar, musamman a cikin birni.
Ya ce kwamitin zai dauki nauyin duba titina, kwatoci da kwalbati da su ka lalace kuma da kuma wadanda suka toshe magudnan ruwa domin a gyara, ko kuma a gina sababbi.
Sannan ya ce kwamitin zai bi duk wasu gine-gine da a ka yi a kan hanyoyin ruwa da suke haifar da ambaliya domin rushe su.
Kwamishinan ya kuma nuna rashin jin dadin da kuma jajanta wa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.
Garba, ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu domin gwamnati za ta tashi tsaye wajen kawo karshen matsalar cikin kankanin lokaci.
A ranar Litinin ne aka tafka mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar, sai dai ruwan ya bar baya da kura inda ‘yan kasuwa musamman a kasuwar Kantin Kwari suka tafka asarar miliyoyin kudi.
Tun farko ‘yan kasuwar sun koka kan yadda suka ce gwamnatin jihar na yin gine-gine ba bisa ka’ida ba a kasuwar.
Sun danganta ambaliyar ruwan da halin ko in kula da gwamnatin jihar ta nuna game da kiraye-kirayensu.