Duk da kiraye-kiraye tare da gargadi da hukumomi daban-daban ke faman yi kan barazanar afkuwar ambaliyar ruwan sama, amma sai aka samu wasu jihohi da kananan hukumomi da dama a fadin wannan kasa da suka yi kunnen uwar shegu ba tare da sun dauki kowane irin mataki ba, wanda hakan ya haifar da samun mummunan ambaliyar ruwa a wannan shekara da muke ciki.
Binciken LEADERSHIP ya tabbatar da cewa, duk da gargadi da jan kunnen da Hukumar NIMET ta yi ta nanatawa, mafi yawancin jihohin kasar nan ba su dauki kowane irin mataki ba, don kaucewa shiga matsalar ambaliyar ruwa a wannan shekara da muke ciki, wanda hakan ya yi sanadiyyar asarar rayuka, gidaje, gonaki da kuma ruftawar manya-manyan gadoji, musamman a Jihohin Bauchi, Gombe, Katsina da kuma Filato.
- Manoman Kenya Na Kara Rungumar Fasahohin Inganta Noma Na Sin
- Takardun Karatun Tinubu Ba Na Bogi Ba Ne – Fadar Shugaban Kasa
Har ila yau, sakamakon karyewa gadoji daban daban da kuma ruftawar wasu daga cikin titina, wasu jihohin sun balle daga Nijeriya, domin kuwa an rasa yadda za a yi a kutsa a shiga cikinsu.
Koda-yake, mafi yawan jihohin ba a samu rahotannin rasa rayuka ko tafka mummunan asara ba, amma duk da haka bincike ya tabbatar da cewa; an rasa rayukan mutum 15 a jihohi hudu da ya hada da Jihar Katsina da ta fi yawan wadanda suka rasa rayukansu da kimanin mutum (10), Kebbi na da (4), Filato (3), Jihar Legas kuma na da (1).
Har ila yau, kwararru daga wasu jihohi da LEADERSHIP ya tuntuba, sun tabbatar cewa suna da kididdiga ta dukkanin abin da ya faru a hannunsu. Sannan Hukumar NEMA ta bayyana mutane sama da 33,000 a jihohi 10 da wannan ifti’la’i na ambaliya ya rutsa da su.
Haka zalika, a farkon wannan shekara ne Gwamnatin Tarayya ta yi gargadin cewa, kimanin kananan hukumomi178 cikin jihohi 32, ciki har da Babban Birnin Tarayya ke fuskantar barazanar afkawa ambaliyar ruwa daga farkon saukar damuna zuwa watan Afrilu, kamar yadda Hukumar NIHSA ta Nijeriya ta yi hasashe.
Tsohon Ministan Ruwa, Injiya Suleiman Adamu ne ya bayyana haka a wajen taron hasashen yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa da aka shirya karkashin jagorancin Hukumar NIHSA ta kasa.
A cewar tasa, jihohin da barazanar ambaliyar ruwan da ake hasashen zai fi shafa su ne, Adamawa, Abiya, Akwa-Ibom, Bauchi, Bayelsa, Benuwai, Kuros-Riba, Delta, Ibonyi, Ikiti, Ido, Gwambe da kuma Jihar Imo.
Sauran jihohin sun hada da Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nassarawa, Neja, Ogun, Osun, Oyo, Ribas, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
“Kananan hukumomi 66 ne ake hasashen za su fuskanci barazanar afkawa ambaliyar ruwan daga watan Afrilu zuwa Mayu da kuma Yuni; inda kananan hukumi 148, su ma ake sa ran za su fuskanci wannan barazana daga watan Yuli zuwa Agusta da Satumba, sai kuma kananan hukumomi 100 daga watan Oktoba zuwa Nuwamba,” a fadin Ministan.
Kazalika, lokacin da ake sa ran dan samun saukin barazanar ambaliyar ruwan zai kasance daga watan Afrilu zuwa Mayu da kuma Yuni a kananan hukumomi 41, sai kuma kananan hukumomi 199 a watan Yuli zuwa Agusta da Satumba, daga nan kuma akwai kananan hukumomi 72 daga watan Oktoba da kuma Nuwamba.
Bugu da kari kuma, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (NEMA) ta fitar da rahoton cewa, wadanda masifar ambaliyar ruwan ta shafa su 33, 983 ne a bangarori daban-daban na wannan kasa a watan Agustan 2023.
Daraktar bincike, tsare-tsare da hasashe, Fatima Kasim ta bayyana cewa, hukamar ta jima tana hada rahotanni kan wadanda wannan iftila’in ambaliyar ruwa ya afkawa watanni bakwai da suka gabata.
Kasim ta kara da cewa, wannan matsala ta ambaliyar ruwa wadda ta saba afkuwa duk shekara, na faruwa ne sakamakon gine-ginen da ake yi ba bisa ka’ida ba. Sai matsalar rashin tsarawa da gina hanyoyi da mugudanan ruwa da kuma rashin kula da harkar shara da sauran makamancinsu.
Kazalika, jihohi 10 ne wadanda iftila’in ambaliyar ruwan ya rutsa da su, sannan mutanen da abin ya shafa kai tsaye 33,983, adadin wadanda suka rasa matsugunansu kuma su 7,353, wadanda suka samu rauni kuma su kimanin 75, wadanda suka rasa rayukansu su kimanin biyar, adadin gidajen da ruwa ya yi awon gaba da su 1,679, gonakin da aka rasa baki-daya kuma 866.”
Bauchi
A Jihar Bauchi, Katsina da Filato gidaje 1,420 ne suka rushe sakamakon wannan ambaliya ta ruwa, Katsina ce ke kan gaba da gidaje 876, Bauchi na biye da ita da gidaje 400, sai kuma Filato da gidaje 150.
Mazauna wadannan unguwanni tare da wasu hukumomi sun shaida wa LEADERSHIP cewa, gidaje 400 da gonaki 300 aka rasa a unguwar Cheledi, Karamar Hukumar Kirfi na Jihar Bauchin sakamakon mamakon ruwan da aka jima ana shekawa.
Haka nan, wadanda wannan iftila’i ya shafa; an sama musu mutsugunai na wucin gadi zuwa wasu daga cikin gine-ginen gwamnati da suka hada da makarantu, gidaje da sauran makamantansu wadanda ambaliyar ba ta shafa ba.
Daraktan Tsare-tsare, bincike da kididdiga na hukumar, Mista Adamu Nayola, wanda ya ba da wannan sanarwa ya ce, sama da gidaje da gonaki 700 aka yi asara a Cheledi.
Haka zalika, al’umma da dama sun yi asarar amfanin gona kamar shinkafa, masara, gero, wake da sauran makamantansu.
Ya kara da cewa, gidaje da gonakin da aka yi asara sakamakon wannan matsala ta ambaliyar ruwa, na alaka kai tsaye da ballewar iyakokin kogi na wannan yanki, sakamakon mamakon ruwan da aka rika tafkawa babu kakkautawa. Nayola, ya bayyana faruwar wannan tashin hankali na ambaliyar ruwa a matsayin mafi muni da ya taba faruwa a wannan shekara da muke ciki.
Ya ce, Kwamishinonin harkokin jin kai, gidaje da muhalli, sun ziyarci wadannan yankuna, domin ganewa idanuwansu wannan barna da ta afku.
“Sun auna tare da yin kiyasin asarar da wannan barna ta ambaliyar ruwa ta haifar a dukkanin wadannan yankuna tare da bayar da gudunmawar da ta dace, domin rage wa wadanda iftila’in ya shafa radadi,” a cewar tasa.
Guda daga cikin wadanda barnar ta shafa a Kauyen Babbaji cikin Karamar Hukumar Zaki a Jihar Bauchin, Jauri Datti; ya roki Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA), ta taimaka ta kawo musu agajin gaggawa, don rage musu radadin wannan annoba da ta rutsa da su.
“Akwai bukatar Jami’an Gwamnati su zo domin tantance asarar da aka tafka, sakamakon wannan ambaliyar ruwa a wadannan yankuna namu, don sanin irin taimako tare da daukin da ya dace a kawo mana,” in ji shi.
A cewar tasa, annobar da ta same mu sakamakon wannan ambaliyar ruwa a wannan shekara (2023), ta ci karo da wani mummunan yanayi na matsalar tattalin arziki da wahalhalu da ake fama da su a wannan kasa, sakamakon cire tallafin man fetir da aka yi tun a watan Yuni, wanda ke kokarin kai ‘yan Nijeriya zuwa kushewa.
Haka nan, shi ma wani daga cikin wadanda annobar ta shafa daga Kauyen na Cheledi, cikin Karamar Humar Kirfi Shamwilu Auwal, ya jaddada cewa barnar da ambaliyar ruwan ta yi a wasu sassa na karamar humar, ba karamin abin tausayi ba ne da tashin hankali. Koda-yake, hukumomi daban-daban daga karamar hukumar sun ziyarci wadanda abin ya shafa ciki har da ‘Yan Majalisar Jiha.
Yayin da LEADERSHIP ya yi kokarin jin ta bakin Adamu Nayola, darakta a SEMA dangane da wannan abu da afku cewa ya yi, ba zai iya cewa komai ba har sai ya samu izini daga wajen sabon Ministan Harkokin Jin Kai da aka nada kwanan nan.
Har wa yau, Karamar Hukumar Zaki da Kirfi; ba su kadai wannan annoba ta ambaliyar ruwa ta shafa a wannan shekara ba, kamar yadda wani Dan Majalisar Jiha ya bayyana kwanan nan a wata tattaunawa da aka shi, ida yake fadin cewa akwai wasu sassan da su ma ke bukatar kulawa wadanda ambaliyar ruwan ta yi wa matukar illa.
Dan Majalisa mai wakiltar yankunan Madara/Chinade, Hon. Dakta Nasiru Ahmed Ala, ya bayyana irin barnar da wannan ambaliyar ruwa ta yi; wanda ya yi sanadiyyar afkawar manya-manyan kwatoci da suka dangana zuwa kauyen Gangai da kuma wasu bangarori na yankunansa.
A wani ci gaba da aka samu, Babban Darakta a Hukumar BASEPA, Dakta Ibrahim Kabir, ya tabbatar da cewa Jihar Bauchi ta kawo wa Kananan Hukumomin Cheledi da Kirfi dauki sakamakon wannan ta’adi na ambaliyar ruwa.
Kabir ya ce, Gwamna Bala Mohammed ya kafa kwamati, karkashin shugabancin Kwamishinan Ma’aikatar Gidaje da Muhalli, Hon. Danlami Ahmed Kawule, da wasu mambobi da suka hada da Kwamishinan Jin Kai, Hajiya Hajara Yakubu Wanka, Darakta Janar na Hukumar BASEPA da kuma Janar Manaja na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar, inda suka ziyarci yankunan da wannan annoba ta shafa.
Binuwai
A Jihar Binuwai, kimanin mutane 473,000 aka yi hasashen cewa wannan annoba ta ambaliyar ruwa ta rutsa da su a wannan shekara da muke ciki.
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na jihar (SEMA), Sir James Iorpuu ya bayyana cewa, a cikin mutum 473,000 da wannan iftila’i ya afkawa, kashi 49.7% mata ne, inda adadinsu ya kama 235,081, yayin da 237,919 ya kunshi maza.
Shugaban Hukumar SEMA, ya bayyana wa al’ummar Tibi cewa, Gwamna Alia, ya umarci wannan hukuma da ke karkashinsa; ta yi hadin guiwa tare da sauran masu ruwa da tsaki na jihar domin rage musu radadin wannan annoba da ta same su, sakamakon wannan ambaliya ta ruwa.
“Barnan da ambaliyar ruwan ta yi a wannan shekara, ta shafi kananan hukumomi 22 cikin 23 da muke da su a wannan jiha, musamman idan aka yi abubuwan da zasu rika kai-komo a tunanin da shi ne, shin me yasa har yanzu kungiyar kwadago ta kasa takawa Gwamnatin Tarayya birki ga dukkan kudurorin ta; musamman abu mafi munin da zai jefa rayuwa cikin mawuyacin hali; cire tallafin man fetur, ace har yanzu babu abin kamawa. Al’amarin nan fa ya fara gundurar yan Nijeriya tare da jawo alamomin tambaya tsakanin Yan Kwadago da Gwamnatin Tarayya- anya ba Danjumma ne da Danjummai ba, musamman irin yadda cikin watanni hudu, kungiyar kwadago ta kasa samar da sauyin da sassaucin rayuwar da ya dace ma’aikata da sauran al’ummar Nijeriya su samu. Saboda hatta tallafin da mafi yawan gwamnatocin jihohi suka raba ba a bai wa ma’aikatan wani abin da zai taka kara ya karya bane.
A wani batu na daban kuma, ba a maganar rassan kungiyar kwadago na jihohi, su kam tun a tashin farko gwamnatocin Suka mayar dasu yan amshin Shata. Saboda hatta karin 25,000 ko 35000 da ake sa ran Gwamnatin Tarayya zata yi, bai shafi na jihohin ba- domin abu ne mai wahalar gaske kungiyar kwadago a matakin jihohi su ce uffan. Sannan kuma gwamnatocin jihohi zai yi wahala su saurari uwar kungiyar ta kasa, kaga kenan sai dai Allah ya jikan ma’aikatan jihohin.
A wata dabaran da Gwamnatin Tarayya ta yiwa kungiyar kwadago shi ne, ta bayyana cewa yajin aikin da kungiyar ta shirya yi ranar 3 ga watan Oktoba, bijirewa umarnin kotu ne, yayin da ita kuma gogar taka; kungiyar kwadagon ta bayyana cewa babu abin da zai taka mata birki a wannan karon, tare da yiwa gwamnati ba’a da cewa: bayan mari kuma harda tsinka jaka, ko kuma ya za a daki mutum kuma a hana shi kuka. Amma dai haka zancen ya wuce, sai dai kuma a jira wani jikon.
Tun da farko, shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) Mista Osita Chidoka, wanda tsohon ministan sufurin jiragen sama ne, ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fara daukar matakai cire harajin bankuna da biyan tsuffin ma’aikata yan fansho.
Mista Osita ya bayyana hakan ne ranar Lahadin da ta gabata a wata hira da gidan Talabijin Channels, ya ce matakan da aka ambata za su taimaka wajen rage wahalhalun da yan Nijeriya ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur, biyo bayan cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar kwadago da Gwamnatin Tarayya a barazanar da suka yi ta bayan nan ta shiga yajin aiki.
A nashi bangaren, Babban Lauyan kare hakkin dan Adam, Mista Femi Falana, ya ce kungiyar kwadagon Nijeriya (NLC) tare da sauran kungiyoyin suna da damar tafiya yajin aikin da gudanar da zanga-zangar kamar yadda suka tsara, yana mai cewa hakan bai zama karan-tsaye ga umurnin kotu ba, sabanin abin da gwamnatin tarayya ta nuna.
Lauya Falana shi ne lauyan kungiyar kwadagon, ya bayar da hujjar cewa babu wata kotu a kasar wadda ta fitar da wata dokar da ta hana ma’aikatan Nijeriya shiga zanga-zangar lumana wadda kungiyar kwadago ke shirin gudanarwa.
la’akari da wadanda suke kusa da gabar teku wadanda suka hada da Makurdi, Guma, Gwer ta gabas, Buruku, Agatu, Katsina Ala da kuma wasu bangarori na Gboko, inda barnar ta fi ta’azzara.”
Katsina
A Jihar Katsina, rahotanni sun tabbatar da cewa an rasa rayuka na kimanin mutum 10, sakamakon afkuwar wannan annoba a wannan shekara da muke ciki.
Mafiya yawan wadanda suka halaka sakamakon wannan annoba, suna tsakanin Sabuwar Unguwar da ke cikin garin na Katsina, mafi munin bangarorin da abin ya shafa a 10 ga watan Yuli, sakamakon rashin magudanan ruwa ne, daga yankunan Kofar Kwaya da kuma Kofar Kura, sakamakon gina babban titi da aka yi (underpass), a yankunan.
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (SEMA), Binta Dangani ta bayyana cewa, wannan hukuma tuni ta yi nazari tare da tantance barnar da wannan annoba ta ambaliyar ruwa ta yi, a Kananan Hukumomi bakwai da suka hada da Katsina, Daura, Dandume, Batagarawa, Mani, Chiranchi da kuma Musawa.
Dangani ta kara da cewa, tuni wannan hukuma ta rarraba kayayyakin gini a matsayin gudunmawa; wadanda suka hada da kwanikan rufi, buhunhunan siminti da kuma katifu kimanin 876 ga wadanda wannan iftila’i ya shafa, domin sake gina mutsugunansu.
Haka zalika, gwamnati ta kashe sama da naira miliyan 50, domin samar da abubuwan da za ta taimaka wa wadannan mutane da ya hada da ba su kulawa ta musamman a asibitoci da sauran bangarori daba-daban.
Kazalika, wani daga cikin shugabannin al’umma na Sabuwar Unguwa Yunusa Rico, ya tabbatar da mutuwar mutum 10 sakamakon iftila’in wannan ambaliya ta ruwa, ciki kuwa har da kananan yara.
Sannan, ya yaba wa kokarin gwamnati na daukar matakin gyaran gadoji da kuma tallafa wa wadanda iftila’in ya shafa ba tare da wani bata lokaci ba.
Filato
A Jihar Filato kuma, Shugaban Yanki na NEMA, Eugene Nyenlong, ya tabbatar wa da wakilinmu rasa rayukan wasu mutane tare da rushewar gidaje sama da 150, a wasu sassa na al’ummar Karamar Hukumar Arewacin Jos na Jihar ta Filato.
Nyenlong ya ce, yankunan da wannan barna ta shafa sun hada Unguwar Rogo, Gangere, Rikkos, Titin Bauchi da kuma Eto-Baba. A cewar tasa, sun dauki adadin yawan gidajen da aka yi asararsu tare da mika rahotannin kai tsaye ga gwamnati.
“Daga rahotannin da muka samu, mutane uku ne suka rasa rayukansu, sakamakon wannan barna ta ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu yankuna namu.”
Haka zalika, wani jigo daga Hukumar NEMA ya roki Gwamnatin Jihar, da ta gaggauta sama wa wadanda annobar ta rutsa da su matsugunai a wadannan yankuna cikin gaggawa.
Kebbi
Ana fara yin ruwan sama a watan Yunin wannan shekara, Jihar Kebbi ta fara fuskantar barnar ruwan sama har karo biyu, inda al’amarin ya faru a garin Zauro da ke Karamar Hukumar Birnin Kebbi ta Jihar da kuma Babbar Shalkwatar Dakingari, a Karamar Hukumar Suru da ke jihar.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, barnar ambaliyar ruwan ta afku ne har karo biyu, inda aka yi asarar gidaje da gonaki da dama a Zauro, sakamakon mamakon ruwan saman da aka samu.
A Dakingari, an samu rahoton mutuwar mutane uku sakamakon yawan ruwan da aka dauki tsawon awanni ana tafkawa.
Gwamna Nasir Idris, ya gabatar da ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan’uwan wadanda suka rasa rayukansa sakamakon afkuwar wannan annoba, yayin da ya ziyarci yankin tare da bayar da gudunmawa ta naira miliyan 40.
Sannan, ya kuma bai wa wadanda suka tafka asara a Zauro tallafin kayan gini, ta karkashin ofishin bayar da agajin gaggawa na jihar.
Neja
A Jihar Neja, Kananan Hukumomi 15 annobar ambaliyar ruwan ya shafa a wannan shekara da muke ciki, wanda ya rutsa da mutum 206.
Rahotan da LEADERSHIP ya samu daga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (NSEMA), rukunin al’ummomi 15 ne suka rasa matsugunansu baki-daya.
Wadanda abin ya fi shafa su ne al’ummar Mokwa, Labun, Lapai da kuma Agaie. Bayanai sun tabbatar da cewa, mamakon ruwan sama tare da ballewar dam-dam da aka fuskanta, su ne suka yi sanadin afkuwar wannan ambaliya ta ruwa.
Akwai akalla sansanin ‘yan gudun hijira 15 a yankunan da ambaliyar ruwan ya fi shafa, amma daga yankin Kede suna karbar agaji ne daga Jihar Kwara.
Sannan, bincike ya tabbatar da cewa, al’ummar Muregi da Gbogifu, na karbar wannan agaji ne kai tsaye daga Patigi a Jihar Kwara, inda al’ummar Chewuya ke zaune a Gakpan duk dai a Jihar ta Kwara.
Wani wanda ya rasa nasa matsugunin a Kauyen Ebogi, yanzu kuma yake zaune a inda ke makawabtaka da Karamar Hukumar Katcha, mai suna Umar Mohammed ya bayyana cewa, “mun rasa komai da muke da shi a halin yanzu da ya hada da gonaki da gidajenmu; wannan ya sa babu wani zabi da ya rage mana illa komawa Katcha mu da sauran ‘yan’uwanmu baki-daya, inda muke a halin yanzu.”
Dalilin da ya sa ba mu zauna a sansanin ‘yan gudin hijira ba, a cewar tasa: “A nan muna iya kokarin yin sana’a, domin samun abin da za mu iya ciyar da kawunanmu, amma a can sai dai mu zuba ido muna jira a taimaka mana, wanda a karshe ba lallai ba ne mu samu wannan taimako ba”.
Koda-yake, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta bayyana cewa, tana ci gaba da tattara adadin wadanda annobar ambaliyar ruwan ta shafa, inda a halin yanzu aka samu kananan hukumomi 15 cikin 25 da ake da su.
Kogi
Sakamakon ci gaba da yawaitar samun ruwan sama a wannan shekarar, ya yi sanadiyyar karuwar ruwan Tekun Neja, wanda hakan ya tilasta wa al’ummar Jihar Kogi yin hijira don kauracewa matsugunansu zuwa wasu wuraren da ban, domin hasashen yiwuwar samun ambaliyar ruwa.
LEADERSHIP ba ta manta da cewa, a shekarar 2022 Jihar Kogi ita ce kan gaba wajen samun matsalar ambaliyar ruwa ba, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa dimbin rayuka, matsugunai da kuma yin awon gaba da gonaki ba.