El-Zaharadeen Umar" />

Ambaliyar Ruwa: Mutanen Katsina Na Neman Dauki…

Matsalar ambaliyar wata masifa ce da ake dakunta a kusan kowace shekara kuma tana zuwa sai dai duk lokacin da ta zo, dole ka ji an yi kuka ko wayau Allah saboda babu lokacin da bata zuwa da asara da ta shafi kodai rai ko kuma dukiya mai tarin yawa ba.

Bisa ga wannan yanayi, gwamnatoci da hukumomi a kowane mataki suna iyakar kokarinsu wajan kara fadakar da jama’a domin gujewa wannan lokaci ko rana, amma dai an ce kaddara Musulmi ta ke fadawa, wannan lokaci kuwa harda da wanda ba Musulmi ba.

Tarihin wannan bala’I ko iftila’I yana da tsawon gaske wannan dalili yasa kodayaushe ake shirya tarurrukan karawa juna sani game da wannan matsala da ke zuwa duk shekara domin dai kawai a samu sauki idan ta zo.

To amma, duk da irin wannan fadakarwa da ake yi kullin mahukunta suna cewa jama’a na bada gudunmawa so sai ta yadda idan wannan iftila’I ya zo ake samun asarar rayuka da kuma ta dukiyoyi.

Haka abin yake a bangaran gwamnati, saboda daukar abin da matukar mahimmaci a matakin jiha da kuma tarayya ana ware makudan kudadai domin a tarbi wannan bala’I ta hanyar bada taimako ga wadanda abin ya shafa, duk da cewa ba haka ake so ba, kanin miji ya fi miji kyau.

A rewacin Najeriya yana fuskantar wannan matsala wadda yanzu takai abin da ta kai, ta yadda duk shekara ana kara samun karuwar rasa rayuka da gidaje da kuma dukiya ta biliyoyin nairori.

Abin tambaya shi ne, me yasa jama’a kullin idan wannan bala’I ya zo, talakawa yake shafa, kuma daga karshe su ake bari da Allah ya yi abin, wannan yasa wasu ke ganin sakacin gwamnati game da tsara birane da kuma bin ka’idar da hukuma ta shinfida akan batun yin gine-gine a cikin birane.

Idan muka duba tarihi, a arewacin Najeriya duk shekara sai ruwa sama ya yi barna, to amma abin tambaya shi ne, haka za a cigaba da zama ba tare da an dauki wani mataki ba, wannan bala’I haka za akyale duk shekara ana asarar dukiya da rayuka?

Muna ganin yadda gwamnatoci a matakin tarayya da kuma jahohi sun ware makudan kudada da niyyar yin wani abu idan haka ta faru, a maimakon a kawo karshen wannan iftila’I, sai da kuma wani lokaci iska mai karfin gaske ce take yin sanadiyar wannan bala’I kafin daga baya ruwa ya sauka.

A gefe guda kuma ana cigaba da fadakar da jama’a cewa, su kiyaye duk wani abu da zai haifar da wannan matsala, ma’ana dai a kiyaye yin gidaje akan hanyar ruwa da ruba shara acikin magudanar ruwa.

Duba da irin barna da ta’adin da ambaliyar ruwa ta yi a jihar Katsina a shekarar da ta gabata a karamar hukumar Jibiya da ke jihar Katsina inda aka samu asarar rayuka kusan 50, wannan lamari ya girgiza masu zuciyar imani, musamman idan ka ziyarci wajan da abin ya faru.

Bisa ga haka, gwamnatoci da hukumomin agaji da masu hannu da shuni sun tausaya sun bada ta su gudunmawa domin rage radadin zafin barnar da wannan bala’I ya yi, daga cikin kuwa har da gwamnatocin wasu jahohi da kuma gwamnatin kasar Nijar.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci jihar Katsina da kansa a madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya jajantawa al’ummar da wannan iftila’I ya afkawa, sannan ya bada sakon shugaban kasa na cewa gwamnati a matakin kasa za su bi diddigin wannan lamari sannan daga baya su bayyana taimakon da za su bada a madadin gwamnatin tarayya.

To amma wani abin mamaki shi ne, har yanzu shiru kake ji kamar an aiki Bawa garinsu, ko me haka ke nufi Allah masani. Amma dai abinda har gobe ake cigaba da tunawa gwamnati shi ne, ta yi alkawari kuma wannan alkawarin yana nan saboda haka ya zama wajibi ta cika shi.

Idan muka dawo akan taimako da neman agaji da mutanen Katsina suke yi yanzu shi ne, an shiga wannan hali tunda yanzu lokacin damina ne, kuma ruwa ya fara kankama musammanan a jihar Katsina.

Kamar kowace shekara a bana ma, wannan bala’I ya ratsa cikin birnin Katsina inda ya yi abinda ya saba wato mummunar barna ga wasu gidajan talakawa, wanda daman na bayyana a matsayin wadanda suke shan wahala idan haka ta faru daga karshe kuma abin ya zama abin tausayi.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a garin Katsina shekaranjiya litinin ya tayar da hankali so sai musamman irin gidajan da suka zube wasu kuma ruwa ya cika su bakil wanda haka ya jawo asarar dukiyoyi masu yawan gaske.

Kofar sauri na daya daga cikin wuraran da wannan bala’I ya shafa, inda har aka bayyana cewa an samu asarar rai guda amma dai har ya zuwa yanzu hukumomi ba su tabbatar da rasa rai ba, sai dai sun bayyana cewa an samu asarar dukiya.

Wannan unguwa ta kofar sauri tarihi ya nuna cewa wuri ne na mahalar ruwa da suke fitowa daga wasu unguwannin cikin garin Katsina inda suke hadewa a wannan unguwa domin fita daga cikin gari, wanda sanadiyar haka wani lokaci yake shafar wadanda suke da makwabtaka da wannan unguwa.

Ambaliyar ruwa dai na shafar tattalin arzikin mutanen wannan yanki, sannan ya tsaida duk wani motsi ko tafiyar da al’amurra a lokacin da aka yi ruwa, sannan yana hana zirga-zirga ga wasu al’ummomi da sai sun ketara ruwa zuwa wasu unguwani da suke makwabtaka da su.

Haka abin ya faru a wasu unguwani cikin birnin na Katsina da suka hada da sabuwar unguwar tudun matawalle da kuma Kofar Kaura tare da Tudun katsira duk acikin birnin Katsina.

Yadda wannan al’amari ya faru akwai ban tausayi kwarai da gaske, domin kuwa iya hangen mutun ruwa ne ya cika gidajan mutane tare da wasu wuraran sana’a da suke da alaka da wadannan wurare.

A bangaran gwamnati musamman ta jihar Katsina wanda an riga an sani duk lokacin da wani abu ya faru makamanci haka tana iyakar kokarin ganin ta yi wani abu domin taimakawa duk wanda abin ya shafi, to sai dai gaskiyar magana shi ne, ba wai gwamnati ta zura ido haka na faruwa ba, daga baya ta zo ta bada tallafi.

Asarar rayuka da ake yi ya kai matuka so sai, saboda haka daukar mataki shi ne abinda ya kamata, domin ko ba komi daman yana daga cikn hakkin da ya rataya akan gwamnati ta kare rayuka da kuma dukiyoyin jama’a.

Akan wannan batu mutanen jihar Katsina suna neman dauki musamman wadanda wannan bala’I ya shafa tun bara, amma har yanzu babu abinda aka yi masu na taimako daga gwamnatin tarayya wanda ta yi alkawarin yin hakan amma shiru kake ji, malam ya ci shirwa.

Sannan dole a kara lalubu wasu hanyoyi da za su taimaka wajan kara wayar da kan jama’a dangane da wannan matsala, ta yadda idan abin ya zo zai iya zuwa da sauki. Da fatan Allah ya kawowa mutanen jihar Katsina dauki game da wannan iftila’i. Amin summa amin.

Exit mobile version