An tabbatar da mutuwar mutane hudu yayin da daruruwan iyalai suka rasa muhallansu sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta mamaye kauyuka 11 a kananan hukumomi biyu na jihar Yobe.
Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe, Dakta Mohammed Goje wanda ya bayyana adadin asarar dukiyoyi yayin da yake karin haske game da ambaliyar a ranar Litinin din da ta gabata, ya ce ambaliyar barazana ce ga daukakin al’ummar Jihar, wacce ta yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.
Kamfanin Jaridar Daily trust ya rahoto cewa ambaliyar ruwan ta biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi a sassa daban-daban na jihar a ranar Lahadi.
“Al’ummomi 11 a karamar hukumar Gulani da Gujba ne bala’in ya shafa, wanda ya yi sanadiyar raba iyalai sama da 100 daga muhallansu.
“Ambaliyar ta yi awon gaba da dabbobi da kayan abinci na miliyoyin naira. Sannan an bada rahoton cewa, mutane hudu sun rasu yayin da wasu da dama suka jikkata,” in ji Gubio.
A halin da ake ciki, Gwamna Mai Mala Buni ya ce gwamnatin jihar za ta kafa kwamitin bayar da agajin gaggawa na kananan hukumomi (LGEMC) domin tunkarar ibtila’i da wuri.