Kasar Afirka ta Kudu ta ayyana dokar ta baci a kasar a ranar Litinin yayin da ambaliyar ruwa ta afkawa larduna bakwai daga cikin tara na kasar, lamarin da ya lalata tituna da gadoji tare da kashe akalla mutane bakwai.
An yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a sassan kasar, kuma ana sa ran za a ci gaba da samun ruwan sama kamar yadda hukumar kula da yanayi ta kasar ta bayyana.
- Badakalar Kudade: Za A Ci Gaba Da Sauraran Karar Da EFCC Ta Shigar Da Matar Gwamnan Kogi
- Ina Goyon Bayan Duk ‘Yan Takarar APC Dari Bisa Dari – Buhari
Sanarwar ta ce gwamnati ta “Ayyana wani yanayi na Iftila’i na kasa don ba da damar daukar matakan da suka dace don magance tasirin ambaliyar ruwa” da ta shafi larduna bakwai, musamman a gabar tekun gabashin kasar.
Cibiyoyin agaji sun ba da rahoton mutuwar mutane bakwai kawo yanzu amma ba a bayyana adadin mutanen kasar ba.
Mutane biyar ne suka mutu a lardin KwaZulu-Natal da ke kudu maso gabashin kasar, in ji Nonala Ndlovu, kakakin hukumar agajin gaggawa na lardin COGTA.
Wani jariri da aka haifa yana cikin wadanda suka mutu, in ji COGTA a cikin wata sanarwa.
Wasu mutane da dama sun bace bayan da suka yi kokarin tsira da ransu.
An bayar da rahoton mutuwar wasu mutane biyu a lardin Mpumalanga da ke arewa maso gabashin kasar, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar.
A arewacin Limpopo, asibiti, tituna, da gadoji sun lalace, yayin da motoci ruwan ya tafi da su.
Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce “A fannin noma, manoma sun yi asarar amfanin gona da kuma asarar dabbobi.”
A bara, Afirka ta Kudu ta fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 400.