• English
  • Business News
Friday, July 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ambaliyar Ruwan Mokwa: Masana Sun Shawarci Gwamnati Kan Matakin Kariya A Nan Gaba

by Abubakar Sulaiman
3 weeks ago
in Labarai
0
Ambaliyar Ruwan Mokwa: Masana Sun Shawarci Gwamnati Kan Matakin Kariya A Nan Gaba
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a garin Mokwa da ke Jihar Neja, ta haifar da fargaba a duk fadin kasar, musamman a jihohi da kuma al’ummomin da hukumar kula da albarkatun ruwa ta Nijeriya, NIHSA ta yi hasashen za a iya kamuwa da cuta. BENJAMIN SAMSON a cikin wannan rahoto ya yi magana da masana kan abin da al’ummomi da gwamnati za su iya yi domin rage sake faruwar lamarin.

Hasashe

A Watan Afrilu ne Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar Muhalli, Farfesa Joseph Utseb, ya gabatar da hasashen ambaliyar ruwa na shekara ta 2025, wanda ya nuna cewa al’ummomi 1,249 a fadin kananan hukumomi 176 a cikin jihohi 30 da Babban Birnin Tarayya (FCT) sun fada cikin wuraren da ake fama da matsalar ambaliya a shekarar 2025.

  • Dalilin Mara Wa Tinubu Baya Ba Tare da Ambaton Shettima Ba – Shugaban APC Na Arewa Maso Gabas
  • Gwamnatin Borno Ta Nemi A Gaggauta Yashe Alo Dam Don Guje Wa Sabuwar Ambaliya

Jihohin da Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya NIHSA ta bayyana cewa suna da hadarin ambaliya, sun hada da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-Riber, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo da kuma Jigawa. Sauran sun hada da Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Ribers, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara.

“A bisa hasashen da aka yi, ana sa ran al’ummomi 657 a yankunan kananan 52 za su fuskanci babban hadarin ambaliya tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni, 500 da 54 a kananan hukumomi 142 tsakanin Yuli da Satumba da kuma 484 a kananan hukumomi 56 daga Oktoba zuwa Nuwamba.

Labarai Masu Nasaba

Majalisar Tarayya Ta Karrama NPA Da Kyautar Gaskiya Da Riƙon Amana Ta 2025

Sojoji Sun Kama Mutum 2 Da AK-47 A Taraba

“An yi hasashen matsakaicin hadarin ambaliya ga al’ummomi 445 a cikin kananan hukumomi 116 daga Afrilu zuwa Yuni, 1,458 a kananan hukumomi 271 daga Yuli zuwa Satumba, da kuma 1,473 a kananan hukumomi 171 tsakanin Oktoba da Nuwamba,” in ji Ministan.

Matakan aiki

Da yake magana da wannan dan jarida, Shugaban Tsangayar Kimiyyar Muhalli na Jami’ar Jihar Nasarawa dake Keffi, Dokta Kante Pkantisawa, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su mai da hankali sosai kan hasashen yanayi da hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NiMET) da NHSA suka yi.

Ya ce, “Ambaliyan da aka yi a Mokwa babbar tunatarwa ce game da tasirin sauyin yanayi da kuma bukatar daukar matakan da suka dace, babu wata fa’ida da ya wuce a ce dole a fadin kasar nan, ya zama al’ummomi da masu ra’ayin su kara taka muhimmiyar rawa wajen hasashen yanayin da NiMET ta yi da kuma hasashen ambaliyar ruwa na shekara-shekara da Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya ta fitar a duk shekara.

“Har ila yau, yana da mahimmanci a gaggauta yashe fadamu da kogunan ruwa da ake da su, tare da hanzarta samar da sabbin hanyoyi don rage kwararar ruwa da barnar da yake haifarwa amma a yi amfani da shi wajen noma.”

Ya bayyana bukatar a ba da shawarwari ga wadanda suka rasa ‘yan uwa da kuma maido da rayuwar ga wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa illa.

“Wannan lokaci ne mafi wahala ga iyalan wadanda abin ya shafa, makwabtansu, da kuma al’ummarsu, zuciyata na kan wadanda suka rasa ‘yan uwansu, tare da dukiyoyinsu, gami da amfanin gona.

“Haka zalika an lalata ababen more rayuwa sakamakon mummunar ambaliyar ruwan, ina addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya sanyaya wa wadanda suka rasa rayukansu, ya kuma rage musu radadin bakin ciki,” in ji shi.

Kudade

Hakazalika, wani mai fafutukar kare muhalli kuma mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Dakta DuroRasak, ya bayyana ambaliyar Mokwa da ta faru a baya-bayan nan a matsayin “mummunan bala’i.” Ya kuma yi kira ga hukumomi da su kara yawan kudaden da ake ware wa muhallin ga jihohin saboda tasirin sauyin yanayi.

“Malalar ambaliyar ruwa da ta afku a Garin Mokwa na Jihar Neja a baya-bayan nan, wani abin tunawa ne mai ban tausayi game da illar rashin kula da muhalli da ababen more rayuwa, da rashin shirye-shiryen bala’i da sauyin yanayi.

“Ambaliyar ruwan da ta afku a sakamakon ruwan sama mai karfi da ya fara tun a ranar 28 ga watan Mayu, ya yi sanadin asarar rayukan mutane da dama tare da jefa al’ummar Mokwa cikin firgici, asara, da rashin tabbas.

“Yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane sama da 200, wasu alkaluma na nuni da cewa adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa sosai, har zuwa 700, saboda yawancin wadanda abin ya shafa sun shiga kogin Neja. Sama da mutane 3,000 ne suka rasa matsugunansu, gidaje sama da 265 sun lalace, an yi asara sama da gidaje 503.

Ya ci gaba da cewa, “Baya ga mace-mace, ambaliya ta yi sanadiyyar raba dubban mutane da muhallansu, ta lalata gidaje, tare da durkusar da tattalin arzikin yankin.

“Yankuna da dama a Nijeriya ciki har da Mokwa na fama da rashin isassun kayayyakin more rayuwa kama daga kan magudanar ruwa, magudanan ruwa da ake da su a lokuta da yawa suna cike da sharar gida, tare da hana kwararar ruwa yadda ya kamata. Gaggawa da fadada birane ba tare da ka’ida ba ya haifar da gine-gine a yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa, wanda hakan ya rage wa kasa karfin shan ruwan da take yi.

“Yanke ciyayi don noma da bunkasa ya rage karfin da kasa ke da shi na rike ruwan sama, da kara kwararar kasa da hadarin ambaliya.

“Gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta kasa su sake duba Asusun Samar da Muhalli da ke tarawa Jihohi, a halin yanzu ya kai kashi 1.0 na asusun tarayya. Ya kamata a kara yawan lamarin idan aka yi la’akari da tasirin canjin yanayi.”

Fadakarwa

A nata ra’ayin, Babbar Jami’iar Kula Da Shirin Raya kasa ta Majalisar Dinkin Duniya, Cibiyar Muhalli ta Duniya, Shirin Ba da Tallafi (UNDP GEF SGP), Misis Ibironke Olubamise, ta bukaci al’umma da su kasance cikin shiri, tare da daukar darussa daga abubuwan da suka faru a baya, kuma kada su yi la’akari da mummunar tasirin ambaliyar ruwa.

“Dole ne mu inganta dabarunmu kuma mu samar da tsare-tsare na ficewa, gami da gano wasu hanyoyin motsi,” in ji ta.

A cewarta, hakan kuma zai taimaka wajen rage matsin lambar da ake yi wa ayyukan bayar da agajin gaggawa idan ambaliyar ruwa ta afku.

Ta kara da cewa “Yana da matukar muhimmanci a tilasta bin ka’idojin tsaro a cikin al’ummomi don tabbatar da cewa mutane sun bi gargadin farko da shawarwarin da hukumomi suka bayar,” in ji ta.

Olubamise ya jaddada cewa Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) za ta iya tallafa wa al’umma ta hanyar samar da kayan agajin gaggawa domin hasashen yiwuwar afkuwar ambaliya, maimakon jira har sai bala’i ya afku.

“Har ila yau, NEMA za ta iya binciken ilimin gargajiya da ayyukan da al’ummomin tarihi suka yi amfani da su wajen shiryawa da sarrafa ruwan sama mai yawa.

“Ya kamata hukumomin da suka dace su hada irin wadannan ayyukan na asali don tabbatar da cewa an watsa sahihan bayanai, kan lokaci, da isassun bayanai ga al’ummomi.”

Karin Nasiha

Har ila yau, wani malami a Sashen Tsare-tsaren Birane da Yanki na Jami’ar Olabisi Onabanjo, Oluwafemi Odunsi, ya ce tsare-tsaren birane da ake da su a Nijeriya sun tsufa, ba a aiwatar da su ba, kuma sun yi nisa da yanayin zamani.

Ya ce, “Manufofin tsare-tsaren biranen Nijeriya suna da cikakkun bayanai a kan takarda, amma tasirinsu ya raunana ta hanyar cin hanci da rashawa, matsalolin fasaha, rashin kudade da kuma rashin aiki na gwamnati, har yanzu muna da matsugunai masu yawa na yau da kullum, masu unguwanni da gidaje masu zaman kansu saboda yawancin garuruwanmu har yanzu ba su da tsare-tsaren ci gaba.

Wadanda ke da tsare-tsaren ba a aiwatar da su ba. Za mu iya yin nuni ga wasu biranen Legas da Abuja.”

Odunsi ya yi nuni da cewa, ba a magance matsalar ambaliyar ruwa yadda ya kamata ba a manufofin da ake ciki yanzu, saboda babu wata dokar kula da ambaliyar ruwa ko kuma hadewa tsakanin tsare-tsare na birane da tsare-tsaren rage hadarin bala’i.

“A halin yanzu, tsare-tsaren tsare-tsare na biranen kasar nan a halin yanzu ba su magance matsalar ambaliyar ruwa ba, sun kafa ka’idoji ne kawai na takaita ambaliya da wuraren da ake fama da ambaliya, wanda wani bangare ke magance haduran ambaliyan ruwa da fallasa. Haka kuma, babau wata doka ta musamman kan ambaliyar ruwa a matsayin tsarin kula da ambaliyar ruwa a Nijeriya.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Ɗan TikTok Tsulange Ya Shiga Hannu Bisa Wanka Da Rigar Mama A Titi

Next Post

Kin Biyan Bashi Daga Wasu Manoma Zai Kawo Cikas Ga Noman Shinkafa A Bana – Ɗan Madamin Samaru 

Related

Illar Kakaba Wa Majalisa Ta 10 Shugabanni Ga Gwamnatin Tinubu – Dattawan Arewa
Labarai

Majalisar Tarayya Ta Karrama NPA Da Kyautar Gaskiya Da Riƙon Amana Ta 2025

8 minutes ago
Sojoji Sun Sake Ceto ‘Yan Matan Makarantar Chibok 2
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kama Mutum 2 Da AK-47 A Taraba

1 hour ago
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa
Labarai

Amurka Ta Rage Wa’adin Bizar ‘Yan Nijeriya Zuwa Wata Uku

2 hours ago
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna
Labarai

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna

3 hours ago
Jihohi 10 Sun Kinkimo Bashin Naira Biliyan 417 Duk Da Karin Samun Kudaden Shiga
Labarai

Jihohi 10 Sun Kinkimo Bashin Naira Biliyan 417 Duk Da Karin Samun Kudaden Shiga

3 hours ago
Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Shirin Ciyar Da Ɗalibai A Makarantun Zamfara
Labarai

Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Shirin Ciyar Da Ɗalibai A Makarantun Zamfara

3 hours ago
Next Post
Kin Biyan Bashi Daga Wasu Manoma Zai Kawo Cikas Ga Noman Shinkafa A Bana – Ɗan Madamin Samaru 

Kin Biyan Bashi Daga Wasu Manoma Zai Kawo Cikas Ga Noman Shinkafa A Bana – Ɗan Madamin Samaru 

LABARAI MASU NASABA

Illar Kakaba Wa Majalisa Ta 10 Shugabanni Ga Gwamnatin Tinubu – Dattawan Arewa

Majalisar Tarayya Ta Karrama NPA Da Kyautar Gaskiya Da Riƙon Amana Ta 2025

July 11, 2025
FRCN Ya Kaddamar Da Shirin Koyar Da Sinanci Mai Taken “Hello China”

FRCN Ya Kaddamar Da Shirin Koyar Da Sinanci Mai Taken “Hello China”

July 11, 2025
Sojoji Sun Sake Ceto ‘Yan Matan Makarantar Chibok 2

Sojoji Sun Kama Mutum 2 Da AK-47 A Taraba

July 11, 2025
Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)

Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)

July 11, 2025
An Fitar Da Sanarwar Beijing Bayan Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adama

An Fitar Da Sanarwar Beijing Bayan Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adama

July 11, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Amurka Ta Rage Wa’adin Bizar ‘Yan Nijeriya Zuwa Wata Uku

July 11, 2025
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna

July 11, 2025
Jihohi 10 Sun Kinkimo Bashin Naira Biliyan 417 Duk Da Karin Samun Kudaden Shiga

Jihohi 10 Sun Kinkimo Bashin Naira Biliyan 417 Duk Da Karin Samun Kudaden Shiga

July 11, 2025
Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Shirin Ciyar Da Ɗalibai A Makarantun Zamfara

Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Shirin Ciyar Da Ɗalibai A Makarantun Zamfara

July 11, 2025
Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista

Shugabannin Jam’iyyar ADC Na Jihohi 36 Da Abuja Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga David Mark

July 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.