Connect with us

KIMIYYA

Amfani 10 Dake Tattare Da Huldar Kasuwanci Ta Intanet

Published

on

Akwai amfain da yawa da masu hurdan kasuwanci za su samu in suna da asususun ajiya na bankin dake hurdasa ta intanet, ko kana nisa da bankin ko ma kana kasar waje matukar kana da waya ko wata na’ura mai shiga intanet zaka yi mu’amalarka ta banki kamar kana cikin bankin da kanka, duk da cewa, amfanin da za a iya cimma yana da yawan gaske amma mun dan tsakulo maku guda 10 daga cinkin irin alfanun da mutum zai iya samu in yana da irin wannan asusun.

  1. Sarrafa Kudinka Cikin Sauki

Zaka samu saukin saffrafa kudadenka, saboda kana da daman sanin halin da asusunka ke ciki a tsawon awanni 24 na rana da kuma cikin kwanaki bakwai na mako, zaka sa ido ka kuma lura da yadda kudi ke shiga da fita cikin asusunka daga duk inda kake a fadin duniya matukar kana da “Serbice” na intanet a in da kake.

  1. Tantance Kudaden Da Suka Shigo Daga Abokan Kasuwancinka Kai Tsaye

Baka bukatar tafiya Banki domin tantance kudin da aka turo maka na wasu kayayyaki da aka saya a shagunanka matukar kana hurda da asusun banki mai “connection” da Intanet, nan take zaka rinka ganin karuwa da raguwar kudadenka a na’uran kwamputar dake gabanka ko ta wayan hannunka ba sai ka shiga darfajiyar bankin ba.

  1. Aika Kudi zuwa Ko ina a Fadin Duniya

Wani alfanun wannan tsarin kuma shi ne, zaka iya aikawa da kudade komai yawansu zuwa masu irin wannan asusun a bankin da kake hurda ko kuma wasu bankin daban kana zaune a cikin dakinka ko cikin ofishinka, shi ma wanda ka aika ma nan take zai ga shigan kudaden cikin asusunsa in yana hurdan banki ne mai intanet.

Hakan na nufin zaka iya aika wa wadanda ka sayi kaya a hannusu daga in da kake ba tare da ka shiga farfajiyar banki ba domin yin haka.

  1. Zaka Biya Kudaden Wasu Harkoki Kai Tsaye.

Biyan kudaden abokan hurda kai tsaye yana daga cikin amfanin da ake samu ta hanyar hurdar Banki ta Intanet, zaka iya biyan kudin kanfanoni irinsu na kudin wuta “NEPA” kudin ruwa “Water Board” da kudin katin waya da katin din “Data Subscribtion” dana kallon tabijin irin su DSTB da Startimes, ko kuma biyan kudaden kasancewarka manba na wasu kungiyoyi da dai sauransu.

  1. Saukin Samun Bayanan Hurdanka na Banki.

Babu wani matsala in har kana son sanin bayanan tarihin hurdan da kayi na banki, nan take zaka san bayana hurdan da kayi daga duk inda kake, bayanai irinsu na ranar da kayi hurdan, lokacin da aka yi hurdan da kuma dalilin yin hurdan, dukkan wadannan bayanan zai zo maka a na’uranka ba tare da bata lokaci ba. Abin da kake bukata shi ne, ka shiga bangaren neman tarihin bayanan hurdan da ka yi, zai fito maka da bayanan dukkan hurdan da kayi gaba daya sai ka zabi wanda kake neman bayani a kai, nan take zai fito maka da tarihin hurdan da kuka yi gaba daya.

  1. Bayanan Matsayin Asusunka

Baka bukatar sai an aiko maka da bayanin matsayin asusunka ta kowace hanya in har kana da asusun banki mai “intanet connection”. Zaka samu cikakken bayanin matsayin kudin da kake da shi a asusunka nan ta ke, abin da kake bukata kawai shi ne na’uran buga takarda domin bugawa musamman in kana bukatar bayanin ne domin wani amfani da shi a wani wuri.

  1. Samun Daman Sanin Kudin Wasu Kayayyaki da Na Wasu Aiyyuka

A kwai wasu harkokin bankuna da sai masu intanet kawai suke iya amfana da su, masu hurda da Banki kai tsaye ba sa samun daman shiga irin wannan harkar. Irin wadannan hurdan sun hada da saukin samun bashi domin ci gaban kasuwancinka da kuma sauki a tsarin da kake bukata na biyan bashin.

  1. Sabunta bayananka Cikin Sauki

Kana bukatar kara sabunta bayanan da ya shafe ka ko na kanfanin kasuwancin ka kuma kana iya yin haka cikin sauki ta hanyar asusun ka mai connection da internet ba sai ka shi ga Banki domin yi haka ba, abin nufi a nan sai ka shiga “account profife dinka ka yi updating kawai”.

  1. Masu Sauraron Matsalolin Masu hurda Na Nan A Kowanne Lokaci.

In ka fuskanci wani matsala da asusunka ko kuma kana bukatar wani bayani a kan abin da ya shafi asusunka, kada hankalinka ya tashi, domin kuwa wani ma’aikacin Bankin na nan a kownne lokaci domin ya warware maka matsalar da kake fuskanta, kana iya kira kai tsaye ko ka aika sakon kar ta kwana kuma nan ta ke za ka samu gamsasshiyar bayani a kan matsalar da ka ke fuskanta.

  1. Hurda mai cikakkiyar Kariya

A hurda banki ta intanet kariya na da matukar mahimmanci musamman ganin cewa, harkar gaba daya ya shafi kudi ne da kuma wasu bayanan na sirri, saboda haka ne ma zaka samu matakan kariya irinsu Log ID da Password da Security number da sauransu, an samar dasu ne domin kare asusun ka daga shigan wani ba tare da izinin ka ba, kuma kana da ikon canzasu a duk lokacin da ka ga dama ko kuma lokaci zuwa lokaci domin kara kariya ga asusun naka.

Harkokin kasuwanci ta kafar intanet sai kara karuwa ya ke yi a ‘yan kwanakin nan, hakan na samuwa ne saboda an samu yawaitar kwanputa da ilimin kimiyya da fasaha, masu kananan harkokin kasuwanci na ta bude irin wannan asusun musamma na ganin bashi da wani tsada kuma yana da saukin hurda, baka bukatar ilimi na musamman kafin ka iya hurda da asusun intanet.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: