Yanayin yadda muke barci, na taka muhimmiyar rawa kwarai da gaske ga lafiyarmu. Haka zalika, bincike ya nuna cewa, barci a gefen hagu; na taimaka wa lafiyar jiki.
Bari mu bincika dalilai guda takwas, wadanda suka sa wannan yanayi na barci a bangaren hagu zai kasance mai fa’ida ko taimaka wa lafiyar jikin Dan’adam.
- Yadda Matuka Jirgi Suka Shantake Da Bacci A Lokacin Sauka
- Ba Na Iya Bacci Saboda Tunanin Budurwata, Me Ya Kamata Na Yi?
1-Abinci na saurin narkewa: Kwanciya da barin hagu na taimakawa wajen saurin narkewar abinci daga kananan hanji zuwa manyan hanji cikin sauki. Sannan, yana taimaka wa dabi’ar tsarin jiki ta yadda zai yi aiki yadda ya kamata tare kuma da hana kumburi da rashin jin dadi bayan cin abinci.
2-Yana rage ciwon zuciya: Ga masu fama da kwannafi ko zafin kirji, kwanciya da bangaren hagu na taimaka masu wajen rage zafin ko hana kwannafin baki-daya tare da masu damar yin barci mai dadi.
3-Taimaka wa lafiyar zuciya: Kwanciya da bangaren hagu na taimaka wa lafiyar zuciwa, musamman wajen aikewa da jini a cikin sassan jikin mutum baki-daya. Haka zalika, kwanciya da bangaren hagu; na inganta wurare daban-daban a jikin Dan’adam tare da rage damuwa a zuciya, musamman ga masu fama da ciwon zuciya ko hawan jini.
4-Yana rage ciwon baya: Ga masu fama da ciwon baya, kwanciya da barin hagu na taimaka musu wajen samun sauki. Kazalika, yana taimakawa wajen samun daidaituwar kashin baya.
5-Taimaka wa mai ciki yayin dauke da juna biyu: Galibi, a kan bai wa masu dauke da juna biyu shawarar kwanciya a bangarensu na hagu, saboda wasu kwararan dalilai. Kwanciya da wannan bangare, na kara yawan gudanar jini zuwa mahaifa tare da taimaka wa jariri wajen yin zagaye. Haka nan, yana kuma taimakawa rage lamba a kan hanta da koda tare da habaka aikin gabobi ga mai juna biyun da kuma jaririn nata.
6-Taimaka wa hanyoyin fitar fitsari da bayan gida: Ko shakka babu, kwanciya da barin hagu na inganta mugudanan ruwan jiki tare kuma da taimakawa wajen fitar fitsari da bayan gida.
7-Yana taimakawa Saifa wajen saurin tace jini: Saifa, tana matukar taka rawa wajen tace jinin Dan’adam, wadda take a bangaren hagu a jikin mutum. Don haka, barci a bangaren hagu; a kara saurin aikin Saifa wajen tace jini, sannan yana kara karsashin lafiya da kuma saurin tace jinn