A kullum na tuna da wakar “Hada Kanmu Afirka Mu So Juna” na marigayi Malam Abubakar Ladan Zariya sai na ji takaicin irin bahallatsar da aka samu a tsakanin kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS), sakamakon kifar da gwamnatocin fararen hula a wadannan kasashen.
Bayan kurar barazanar daukar matakin sojin ECOWAS a kan Nijar ta lafa, a watan Janairun bana, Mali da Burkina Faso da kuma Nijar suka fito karara suka yi fatali da tayin sake dawowa ECOWAS tare da kafa wani hadin kasashensu da suka zartar tare da rattaba hannu a ranar 6 ga Yulin 2024.
- Google, Microsoft, TikTok Sun Biya Gwamnatin Nijeriya Harajin N2.55trn A 2024 – NITDA
- Gobara Ta Kone Shaguna A Kasuwar Yobe
Wannan ya sake karya lagon fatan da ake da shi na sake dunkulewar ECOWAS tare da hada karfi da karfe a tsakanin mambobin kasashen wajen fuskantar matsalolinsu na ci gaban tattalin arziki da kyautata zamantakewa. Saboda kasashen uku suna zargin ECOWAS da zama ’yar amshin shatar kasashen yammacin duniya da suka raba-gari da su musamman uwargijiyarsu Faransa.
Masana da masharhanta a yankin Afirka na ci gaba da yekuwar a lalubo bakin zaren sulhu a tsakanin ECOWAS da kasashen. Wannan ya sa hankalina ya karkata ga wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da wata kafar yada labarai ta kasar Sin CGTN ta gudanar game da irin tasirin da salon diflomasiyyar kasar Sin ya yi wajen sulhunta kasashen da suka yi baram-baram da juna.
Kowa ya san an kwashi tsawon lokaci ana gaba tsakanin kasashen Saudiyya da Iran, duk kuwa da irin kusancin da suke da shi da juna na zama kasashe masu alkibla daya ta musulunci da kasancewarsu ’yan yankin Asiya. Amma bisa amfani da salon diflomasiyya ta kasar Sin, kasashen biyu sun sake amincewa da juna har ma suka yanke shawarar mayar da huldar diflomasiyya a tsakaninsu a ranar 6 ga watan Afrilun 2023 bayan wata ganawa a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Haka nan, shekara daya bayan sulhun Iran da Saudiyya, bisa amfani da salon diflomasiyyarta, kasar Sin ta yi nasarar sake sulhunta bangarorin Falasdinawa na Fatah da Hamas da suke zaman ’yan marina a tsakaninsu ta yadda za su zama tsintsiya madaurinki daya su kuma fuskanci kalubalen yankin Falasdinu bai-daya.
Hakika sulhunta gabar da ta shafi akida ba karamar nasara ba ce saboda kowa ya san yadda ake zafafa ta a tsakanin bangarorin da ake yi. Bisa wadannan manyan nasarori da salon diflomasiyyar kasar Sin ya samu baro-baro a fili, ko shakka babu idan aka yi amfani da hakan za a iya daidata hannun-rigar da kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso suka yi da ECOWAS. Musamman ganin cewa kowane bangare a cikinsu ya amince da kasar Sin a matsayin mai taimako da kawo alheri ga Afirka.
Kuma ba ni kadai nake ganin haka ba. A binciken jin ra’ayoyin da CGTN ta yi game da tasirin salon diflomasiyyar kasar Sin, mutane daga sassan duniya daban-daban sun ba da tabbacin irin tasirin da salon diflomasiyyar kasar Sin ya yi wajen kawo kwanciyar hankali a duniya.
Bari mu kawo misalai daga shirye-shiryen da kasar take kawo shawarar aiwatarwa ta hanyar diflomasiyya a tsakanin kasashen duniya domin samun ci gaba na bai-daya. Daga cikin alkaluman da aka tattaro, kaso 82.5 cikin dari na wadanda aka ji ra’ayoyinsu sun ce tsarin da kasar Sin ta zo da shi mai taken “al’umma mai makomar bai-daya domin bil’adama” ya kara zaburar da kokarin gina kyakkyawar makoma ga dan Adam.
Haka nan kaso 84.5 cikin dari na masu bayyana ra’ayin sun aminta da shawarar Shawarar Bunkasa Ci Gaban Duniya, inda suka yi amannar cewa samar da ci gaba ita ce hanyar warware matsalolin duniya da samun farin ciki ga dan Adam. Duk wadannan shawarwari daga cikin hikimomin salon diflomasiyya ne na kasar Sin.
Don haka, amfani da salon diflomasiyyar kasar zai ba da damar warware takaddamar da ake yi tsakanin ECOWAS da kuma kasashen da suka yi bara’a da ita su uku. (Abdulrazaq Yahuza Jere)