Connect with us

RAHOTANNI

Amfanin Awon ciki Ga Lafiyar Uwa Da Ta Jariri

Published

on

Wani kwararren likita a asibitin Sir, Sanusu da ke unguwar ‘Yan kaba a garin Kano Dakta Salisu Muhammad, ya nuna muhimmancin da ke tattare da zuwan mata masu ciki asibiti domin duba lafiyarsu da ta abin da suke dauke da shi, da kuma ci gaba zuwa asibitin bayan haihuwa.

Likitan ya yi bayanin cewa, awon ciki na nufin kula da lafiyar ciki, tare da bincike a kan alamomin da za su iya shafar lafiyar jariri daga jikin uwa, domin a magance su, kamar alamomin ciwon suga da hawan jini ga mai ciki domin a ba ta magani  domin a samu cikakken bayanin lafiyar uwa da ta abin da za ta haifa. An kasa lokacin awon ciki zuwa lokuta biyu; akwai lokaci na farko da mai ciki za ta fara zuwa asibiti da kuma lokaci na biyu lokacin da za ta ci gaba da zuwa, bayan zuwanta na farko.
Mata da yawa kan sha matsananciyar wahala  lokacin da za su haihu. Wasu da yawa sukan rasa jariran da za su haifa, wasu ma  sukan mutu, sakamakon rashin zuwa awon ciki. Idan mai ciki na zuwa awo kamar yadda ya kamata jaririn da ke cikinta zai tsallake kasadar kamuwa da wasu cututtuka, sannan ita ma uwar za ta tsira daga wasu haduran da ke tattare da lokacin haihuwa.
Saboda haka, yana da matukar muhimmanci, a wayar da kan mata masu ciki a kan muhimmancin zuwa asibiti lokacin da mace ta samu ciki.
Ma’anar Awon Ciki
Awon ciki na nufin kula da lafiyar mai ciki da kuma jaririn da za ta haifa tun daga lokacin da ta samu ciki har zuwa lokacin haihuwa.
Haka kuma zuwa awon cikin na nufin zuwa asibitin da mai ciki kan yi a jere kamar yadda yake a ka’aida  domin duba lafiyar cikin da kuma bincike a kan wasu alamomin cututtuka ga mai ciki, wadanda za su iya  shafar lafiyar jariri domin a magance cutar da aka gano alamomin na su ga mai cikin. Hakan na taimaka wa wajen bayar da cikakken bayani kan lafiyar uwa da ta abin da ke cikinta, yadda za a kauce wa matsaloli lokacin haihuwa.
Duba lafiyar ciki aiki ne da kwararrun likitoci a wannan fannin  kan yi ga mata masu ciki, domin a tabbatar da lafiya mai ciki da kuma ta abin da za ta haifa.Wato kula wa ta musamman da kwararrun ke yi ga mai ciki domin a dinga tabbatar da matsayin lafiyarta da ta cikinta daga lokaci zuwa lokaci.
Amfanin Awon Ciki
Awon cikin na taimaka wa inganta lafiyar jaririn lafiyar da za a Haifa.
Awon ciki na sa a gano tare da magance cututtukan da ka iya shafar jariri daga uwa kamar, ciwon suga da hawan da sikila da sauran cututtuka.
Awon cikin na taiamaka wa a gano hanyar da za a bi wajen magance manyan matsalolin da za su shafi lafiyar uwa da ta jaririn da za a Haifa.
Yana taimaka wa mata masu ciki su san yadda za su yi tattalin cikinsu da kuma jaririn da za su haifa.
Yana taika wa wajen ilimantar da mata yadda za su raini ‘ya’yansu.
Yana ilimantar da mata kan yadda za su fahimci wasu alamomin wasu matsaloli da kuma yadda za su magance su kamar; yawan ciwon kai da ciwon ciki da zubar jini da sauran su.
Yana taimaka wa mata yadda za su fahimci amfanin tazarar haihuwa da kuma hadarin da ke tattare da daukar ciki.
Yana ba mata masu ciki cikakken bayanin abinci da ya kamata su dinga ci.
A wajen awon ciki ana yi wa mata allurorin riga-kafi, kamar allurar riga-kafin tetanus.
Ana ilimantar da mata yadda za su shayar da jarirai.

Yana taima wa mata masu ciki yadda za su kula da cikinsu da kuma lokutan da za su dinga yin allura.
Yana samar da hanyar da mata za su amfana da wasu magunguna kyauta, kamar maganin maleriya da na cutar kanjamau.
Yana taimaka wa mata sanin abin da ya kamata su yi lokacin nakuda da kuma inda ya kamata su haihu.
Yana taimaka wa mata masu ciki su dauki matakin kan yawan amai da zafin kirji.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: