Connect with us

Ka San Jikinka

Amfanin Bi-ni-da-zugu Ga Dan’adam

Published

on

Bishiyar  Bi-ni-da-zugu ana kiranta da sunaye daban-daban a sassan duniyan nan dangane da yadda al’umma suka santa da shi bisa tsarin al’adarsu. A wasu wuraren ko ƙasashe ana kiranta, pignut, ko purge nut, ko Barbados nut, ko kuma Black bomit nut. A ƙasashen Asiya kuma musamman ma ƙasar India, a yawa-yawan lokaci ana ƙiran bishiyar da ‘Castor oil plant’ ko kuma ‘hedge Castor oil plant’  A Nijeriya kuma, al’ummar Hausawa na ƙiranta Bi-ni-da-Zugu, ƙabilar Igbo kuma suna kiranta da Olulu idu ko Owulu idu. ƙabilar Yoruba kuma suna kiranta Botuje, ko lapa lapa fun fun. Ya yin da ƙabilar Fulani kuma ke kiranta da kwalkwalaje a harshensu na Fillanci.

Tsarin Bi-ni-da-Zugu

Bi-ni-da-zugu, shi dai bishiya ne wanda dangane da tsarinsa, yayin da ya girma matuƙa, yana kai kimanin mita 3-4 ko kuma 3 zuwa 8 na tsawo. Daga cikin zuri’arsa akwai ire-irensa kusan kimanin ɗari biyu da tamanin da uku (283) da wasu nau’ukan tsirrai ko shuka da suka kai kimanin dubu bakwai da ɗari uku, waɗanda suke iri guda a duk faɗin duniyar nan a mabambantan yankuna waɗanda yanayinsu ya bambanta. Shi dai Bi-ni-da-Zugu, dangane da yanayi,  buƙatar fari (rashin ruwa) amma kuma an iya shuka shi ko yana iya tsira a sahara ko rairayi, sannan yana iya tsira ko fita a ko ina yake kuma a kowane iri nau’i na ƙasan shuka, ko a taɓo ko yashi ko a inda duwatsu suke don bai damu da ko akwai fari ba (rashin ruwa) sannan yana iya rayuwa kusan shekaru hamsin (50), sannan kuma babu wani ƙwaro da ke addabarsa balle ya masa illa.

Bishiyar Bi-ni-da-zugu na da gajerun gaɓa na jikinsa sannan yana da rassa daga jikin kowane gaɓa na shi. Sannan bishiya ne da jikinsa ke da laushin gaske kuma fatar jikin bishiyar na nan kore-kore da wani ɗan layi fari-fari a jiki. Dangane da tsarin ganyensa kuma, ganye ne falafala ba su da tsayi sai faɗi wanda faɗin ya kai kimanin 2 – 6 mm. Sannan ganyen kan canja launinsa a wasu lokuta zuwa wani launi na rawaya, sannan kuma furen bishiyar Bi-ni-da-zugu yana da launi kore-kore da rawaya wanda faɗi da tsayin furen ya kai 6 – 7 cm sannan yana da ganye guda biyar a jikin furen.

Yanayinsa

Dangane da yanayi, Bi-ni-da-zugu ana iya samunsa a layin da yake a latitude na 23026. Sannan yana buƙatar zafi ko dayake yana iya jure zuban dusan ƙanƙara a matsakaicin yanayi. Bi-ni-da-zugu na daga cikin zuri’ar  pantropical duk da yake yana da alaƙa  da guri mai mai yanayin zafi da ruwa, amma yana bunƙasa a kowane ɓangare na ƙasashen Afirka da na Asiya.

Wasu alfanun Bi-ni-da-zugu

Itacen da kuma ‘ya’yan itatuwan Bi-ni-da-zugu za a iya amfani da su a wurare daban-daban a ɓangarori da dama har ma a matsayin makamashin wuta.

Da farko, ɗan itacen na ɗauke da wani mai da ake kira biscous oil wanda nauyinsa ya kai (0.50%) wanda ake sarrafa su wajen samar da candles da kuma sabulu a ma’aikatar da suke samar da sarrafa kayan kwalliya na shafawa a fuska ko a jiki.

Ana yin amfani da itacen wajen dafa abinci ko a yi amfani da shi domin ya haskaka wuri a matsayin diesel ko paraffin (wani mai ne da ake samu daga cikin man fetur).

Bi-ni-da-zugu na taimaka wa sinadarin organic (wanda ya shafi abin da abubuwa masu rai suka samar a ƙasa) kamar tana (earth-worm) wanda yake ƙara inganta darajar ƙasa (soil).

Bi-ni-da-zugu in ya tsira a wuri yana taimakawa wajen magance matsalar zaizayar ƙasa (soil erosion) da gusar da tarin ƙasa, daga fari (drought).

Ana kuma amfani da itacen Bi-ni-da-zugu wajen iyakance yanki (boundary fence)

Ana kuma amfani da ‘ya’yan itacen Bi-ni-da-zugu a matsayin maganin ƙwari, kamar farin ɗango da kuma gara, sannan ganyen na warkar da murar dabbobi, sannan kuma furannin itacen abin sha’awa ce ga ƙudar zuma. Sannan kuma ɓawon itacen ana amfani da shi wajen samun sinadarin sauya launin tufa kamar blue dye, gray dye, purple dye.

Biyo bayan abin da aka ambata a baya da suka jiɓanci alfanun Bi-ni-da-zugu ya sanya al’ummar karkara zantawa domin binciko wa kan su makamashi da zai maye gurbin wanda suke amfani da shi wato fossils fuels (tsiro da ta rayu shekaru masu yawa da suka wuce, wacce aka kiyaye ta ajikin dutse).

To waɗannan da ma wasu da ba alissafa ba na daga cikin alfanun da ake samu daga itacen Bi-ni-da-zugu.
Advertisement

labarai