ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, July 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amfanin Manhajar Gmail A Wayoyin Hannu

by Sulaiman and Ibrahim Sabo
4 years ago
Gmail

Kamar yadda bayani ya gabata, Gmail daya ne daga cikin ’email service provider’ da kamfanin Google ke gudanar da shi.Ga mai amfani da wayar Android ‘email’ na kamfanin Google (Gmail) zai fi yi masa amfani fiye da sauran ‘probiders’ irinsu Yahoo, Hotmail, Yanded da sauransu.

Da yawan mutane in an ce Google, sukan takaita shi da ‘searching engine’ ma’ana wurin da za ka yi browsing (bincike) na wani abu; in kuma aka ambaci ‘Gmail’, da yawa mukan takaita aikinsa da turawa ko karbar ‘email’ da ajiye lambar waya; amma duk amfaninsa ya wuce nan.

  • Mai Damfara Da Sunan Mace A Facebook Ya Shiga Hannun ‘Yan Sanda A Kano

Google shi ne kamfanin da yafi kowanne kamfani karfi a duniyar fasahar sadarwa. Shi ne kamfani da yake gudanar da OS (operating system) na Android tare da shi da sauran wasu kamfanoni. Android shi ne OS da mafi yawancinmu muka fi amfani da shi a wayoyinmu na Samsung, Pidel, Tecno, Infinid, Itel, Diomi, Gionee, Huawei, HTC, Motorola, Oppo, Nokkia, Bibo da sauransu.

ADVERTISEMENT

1. Idan ka bude ‘Gmail Account’ kai tsaye ka yi rijista ne ‘Google account and serbices’, ma’ana zaka yi amfani da duk wani tsare-tsare da ‘manhajojin 131’ da Google ke gudanar da su (about.google/products), wadanda iya mai Google account ne kadai zai iya morarsu kai tsaye 100%.

Wadannan manhajojin sun hada da Gmail, Playstore, YouTube, Google Dribe, Photos, Blogger, Forms, Alerts, AdSense, Google Chats, Google classroom, Family Link, Find My Debice, Google Groups, Contacts, Message, Google one, Podcast, Hangouts, Scholar, Meet, AdMob, Cloud, Translate… da sauransu.

LABARAI MASU NASABA

Birtaniya Ta Yaba Wa Tinubu Kan Sauye-sauyen Tattalin Arziki

Jihohi 28 Da Abuja Na Fuskantar Hadarin Ambaliyar Ruwa —Rahoto

Kuma ana amfani da su wajen tura sakonni, karatu, kasuwanci, debeloping, taruka, adana bayanai, kididdiga da sauransu.

2. Mallakar ‘Google account’ yana taimaka wa wajen Auto-Fill na Login Credentials (bayanai da zaka shiga domin bude wani shafi, wato (username da password); ma’ana, idan ka yi sabing bayanan shiga wani shafi (kamar Facebook ko Twitter), babu bukatar sai ka yi typing na ‘username da password’, a’a kai tsaye Auto-Fill zai shigar maka da bayanan.

Ba za mu iya bayanin dukkan ‘Manhajoji 131′ ba a yanzu, ba kuma lalle a ce sai ka iya amfani da dukkanin manhajojin ba (ya danganta da wanda kake bukatar amfani da shi), sannan wasun su ba a iya amfani da su a wasu kasashen.

Ga bayanin wasu a takaice:
PLAYSTORE– rumbu ne mai dauke da manhajojin Android (apk) 2.59 million (Statista, 2022). Mai Google account (Gmail) ne kadai zai iya shiga domin sauke ‘apps’ daga cikin Play store.
GOOGLE CONTACTS – ‘app’ ne da ake iya adana lambobin waya daga 1 zuwa 25,000. Amfani da ‘Google Contact’ na da matukar muhimmanci, saboda ko an sami akasi wayarka ta bata, ko lalace, ko aka sace, da zarar ka sami wata wayar ko a computer za ka iya dawo da duk ‘lambobin wayarka’ da ka adana (sabing) a cikinsa.

BLOGGER– zaka iya kirkirar ‘blog site’ da Blogger, har kana iya wallafa rubutu kyauta. Idan kana samun traffic da yawa, za ka iya ‘rijista’ da ‘AdSense’ ka fara samun kudin da Blogger din, musamman idan kana dora talla/ads (misali, leadership.blogspot.com).
FIND MY DEVICE – manhaja ce da za ta taimaka wajen gano inda wayarka take, idan ka rasa ta, ko ka jefar, ko aka sace.
YOUTUBE – wannan sananne ‘app’ ne na Google da zabka iya bude ‘channel’ da shi ta hanyar amfani da ‘Google Account’. Idan kana samun traffic da yawa, akalla subscribers 1000. kuma aka samu an bude ‘contents’ na ka kamar sau 4000, za ka iya fara samun kudi da YouTube.
GOOGLE PHOTOS – Wannan manhajar tana taimaka wa sosai wajen adana hotunan cikin waya. Idan kana ‘backup’ na hotuna a cikin ‘Photos’ za a iya ‘restoring’ nasu a kowace irin waya ka canza, a kowane lokaci.

GOOGLE DRIVE – wannan manhajar ‘cloud’ ce da ke iya bawa mutum damar ajiye ‘files’ a ciki. Suna bawa kowane user (mutum) ‘storage’ na 15 gigabytes. Zabka iya bude abubuwa da ka adana a cikin Dribe a kowace waya ko computer idan ka yi amfani da ‘Google Account’ (Gmail) naka.

SCHOLAR – Google scholar kamar ‘Google searching engine’ ne. Yana taimaka wa wajen lalubo metadata (ta rubuce-rubuce na ilimi).
Misali, idan ka sami wani rubutu, kuma kana son ba shi ‘reference’ idan ka dauki ‘jumla’ ka dora a scholar zai baka irin wannan jumlar ta bayyana a rubuce-rubuce da suka gabata, cikin littattafai, ko mukala (articles), ko journals, ko mujalla da sauransu.

CHROME REMOTE DESKTOP – manhaja ce da zata baka damar shiga cikin files na computer daga wayarka, ko da ba ka tare da computer din.
GOOGLE ADS – Manhajar AdSense da AdMob na taimaka wa masu amfani a social media yin rijista domin samun kudi ta hanyar dora talla a shafukansu (ads).
MEETS – Kamar zoom yake, ana iya yin meeting online.

Akwai sauran apps na Google da za su taimaka sosai wajen debeloping, kamar optimize, Google Analytics, Google Cloud, Firebase, Flutter, Play Protect, Play Games, Surbey, Web da sauransu.
Akwai apps na Google da za su taimaka wajen editing na hoto, SNAP SEED da PHOTOS. Akwai na duba taswira (map), GOOGLE MAP da GOOGLE EARTH. Akwai manhajar karbar bayanai ta GOOGLE FORMS, akwai manhajar fassara ta TRANSLATE. Akwai manhajoji da yawa na GOOGLE, sai a hankali ko in bukata ta tashi, za mu dauki wasu muna bayaninsu a takaice.

ABIN LURA:
1. Yawancin wadancan tsare-tsare na Google, iya masu Google account (Gmail) ke iya morarsu 100%.
2. Ana iya amfani da Gmail, kamar sauran ‘probiders’ (Yahoo, Hotmail…) wajen yin rijista ko cike-ciken da ake yi a yanar gizo, kamar bude profile na makaranta ko cike aiki (job application), ko cike tallafi, misalin, surbibal fund da sauran cike-cike.
3. Kar ka yi gangancin bawa kowa Login details na Gmail naka, domin za a iya shiga (accessing) dukkan wadancan tsare-tsaren da shi.

Gmail
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Ofishin Jakadancin Sin A Nijeriya Ya Shirya Taron Murnar Cika Shekaru 99 Da Kafuwar Rundunar PLA Ta Sin
  • Sulaiman
    Farfesa Dr. Otto Heinrich Herzog: Sin Tana Da Tsari Mai Kyau Na Aiwatar Da Dabarun Ci Gaba
  • Sulaiman
    An Watsa Shirin Talabijin Mai Taken “Yiwu Ta Duniya –Yadda Xi Jinping Ke Kulawa Da Jagorantar Ci Gaban Yiwu”
  • Sulaiman
    Baya Ga “Sanyi Irin Na Sin”, Akwai Wasu Abubuwa Da Yawa Da Masu Yawon Bude Ido Na Turai Ke Sha’awa Kan Kasar
Gmail
Ibrahim Sabo
+ posts Bio
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Sabuwar Hanyar Kwacen Shafin Facebook (II)
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Sabuwar Hanyar Kwacen Shafin Facebook (I)
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Mene Ne Tsarin 5G?
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Yadda Ake Sarrafa Rubutu Ta Word-Processing

MASU ALAKA

Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Rahotonni

Birtaniya Ta Yaba Wa Tinubu Kan Sauye-sauyen Tattalin Arziki

July 25, 2026
Kogin Kumadugu Ya Yi Ambaliya Karon Farko Cikin Shekara 100 A Yobe
Rahotonni

Jihohi 28 Da Abuja Na Fuskantar Hadarin Ambaliyar Ruwa —Rahoto

July 25, 2026
NLC Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Yajin Aiki Kan Albashi Mafi Karanci
Rahotonni

NLC Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Yajin Aiki Kan Albashi Mafi Karanci

July 24, 2026
Next Post
Ya Halatta Mu Zubar Da Ciki Ni Da Mijina Idan Likita Ya Gaya Mana Yaron Da Za Mu Haifa Sikila Ne? (Fatawa)

Ya Halatta Mu Zubar Da Ciki Ni Da Mijina Idan Likita Ya Gaya Mana Yaron Da Za Mu Haifa Sikila Ne? (Fatawa)

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Birtaniya Ta Yaba Wa Tinubu Kan Sauye-sauyen Tattalin Arziki

July 25, 2026
Ofishin Jakadancin Sin A Nijeriya Ya Shirya Taron Murnar Cika Shekaru 99 Da Kafuwar Rundunar PLA Ta Sin

Ofishin Jakadancin Sin A Nijeriya Ya Shirya Taron Murnar Cika Shekaru 99 Da Kafuwar Rundunar PLA Ta Sin

July 25, 2026
Sabon Rahoton Bankin Duniya Ya Yaba Da Yadda Tattalin Arzkin Nijeriya Ke Bunkasa

Sabon Rahoton Bankin Duniya Ya Yaba Da Yadda Tattalin Arzkin Nijeriya Ke Bunkasa

July 25, 2026
Farfesa Dr. Otto Heinrich Herzog: Sin Tana Da Tsari Mai Kyau Na Aiwatar Da Dabarun Ci Gaba

Farfesa Dr. Otto Heinrich Herzog: Sin Tana Da Tsari Mai Kyau Na Aiwatar Da Dabarun Ci Gaba

July 25, 2026
Yadda Ake Faten Dankalin Turawa Da Kaza

Yadda Ake Faten Dankalin Turawa Da Kaza

July 25, 2026
An Watsa Shirin Talabijin Mai Taken “Yiwu Ta Duniya –Yadda Xi Jinping Ke Kulawa Da Jagorantar Ci Gaban Yiwu”

An Watsa Shirin Talabijin Mai Taken “Yiwu Ta Duniya –Yadda Xi Jinping Ke Kulawa Da Jagorantar Ci Gaban Yiwu”

July 25, 2026
Baya Ga “Sanyi Irin Na Sin”, Akwai Wasu Abubuwa Da Yawa Da Masu Yawon Bude Ido Na Turai Ke Sha’awa Kan Kasar

Baya Ga “Sanyi Irin Na Sin”, Akwai Wasu Abubuwa Da Yawa Da Masu Yawon Bude Ido Na Turai Ke Sha’awa Kan Kasar

July 25, 2026
Rodri Ya Amince da Tayin Komawa Real Madrid

Rodri Ya Amince da Tayin Komawa Real Madrid

July 25, 2026
Ministan Harkokin Wajen Sin Wang Yi Ya Yi Kira A Karfafa Hadin Gwiwa Na Kut-Da-Kut A SCO Domin Gina Duniya Mai Damawa Da Mabambantan Bangarori

Ministan Harkokin Wajen Sin Wang Yi Ya Yi Kira A Karfafa Hadin Gwiwa Na Kut-Da-Kut A SCO Domin Gina Duniya Mai Damawa Da Mabambantan Bangarori

July 25, 2026
Kalolin Kitso Na Zamani: Yadda Ake Yin Fulani Style

Muhimmancin Kula Da Gashi Domin Lafiyarsa Da Kyawunsa

July 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.