Xender manhajar ce da muka fi sani wajen yin aikawa da karbar sako wato ‘transfer’ na ‘files’ (videos, audios, photos, applications da sauransu) daga wata wayar zuwa wata waya daban.
A tsakanin Android da Android, ko Android da iPhone, ko tsakanin Androi da KaiOS, ko kuma tsakanin waya da computer.
Akwai kuma wasu muhimman aiyuka da za mu iya yi da Xender wandanda suka hada da:
1. Sauke status na WhatsApp
2. Sauke ‘bideo’ daga Facebook, Twitter da Instagram
3. Conberting na ‘bideo’ zuwa ‘Audio’
4. Mayar da kayan (files) na tsohuwar waya zuwa sabuwar waya (cloning)
Yadda Ake Sauke Status (Bideo ko Photo) daga WhatsApp
Kafin ka sauke ‘status’ na WhatsApp ta hanyar amfani da Xender, sai ka bude (status biewing) ta WhatsApp da farko tukunna, sai ka shiga cikin Xender, ka duba can kasa, za ka ga ‘social’, sai ka shiga ‘social’. Duk ‘status’ din da ka bude za su fito a nan, sai ka zaba, ka yi ‘sabing.’
Yadda Ake Sauke Bideo Daga Facebook, Twitter Da Instagram
Idan kana bukatar sauke (downloading) na wani ‘bideo’ daga Facebook, Twitter ko Instagram ta hanyar amfani da Xender ga matakan da zaka bi:
• Za ka yi ‘copy’ na link din wannan bideon.
• Sai ka bude Xender, ka shiga wannan wajen na ‘SOCIAL’
• Sai ka shiga wajen da aka rubuta ‘PASTE AND DOWNLOAD’, sai ka bude, ka yi ‘paste’ na wancan link da ka yi copied din. Wato ka danne ya tsanka a wajen, za ka ga link din ya sauka.
• Zai yi ‘analyzing’ na link din na lokaci kadan, sai kuma ya fara sauka (downloading).
Yadda Ake Mayar Da Bideo Zuwa Audio (Conberting) A Xender
Ana iya amfani da Xender wajen mayar da bideo na kallo, zuwa audio na saurare. Wato ‘conberting’ na ‘bideo’ ya koma ‘audio’ ta wadannan matakan:
• Ka shiga cikin ‘Xender’
• Ka duba daga kasa, za ka ga wani waje ‘bottom’ an rubuta ‘ToMp3’, sai ka shiga ciki.
• A ciki, zai baka zabi guda biyu. Na farko, ToMp3, na biyu kuma LOCAL. Za ka iya shiga ta kowannensu, don nemo ko zabar bideon da kake son mayar wa Mp3 din (audio).
Mayar Da Kayan (Files) Na Tsohuwar Wayarka Zuwa Sabuwar Waya
Idan ka canza wayarka, wato ka sayi sabuwar waya, kuma kana so ka ka kwashe abubuwan ka na kan tsohuwar wayar taka, to ana amfani da Xender cikin sauki wajen kwashe su.
Xender tana da tsarin CLONE, tsari ne da zai baka damar ‘transfer’ na ‘files’, applications, contacts da sauransu, daga wata wayar zuwa wata wayar.
Wannan tsarin na CLONE zai ba ka damar debe kayan tsohuwar wayarka, zuwa sabuwa ba tare da ka rasa komai ba, ciki har da ‘messages’ da ‘call history’.
Yadda zaka yi amfani da wannan tsarin na Xender CLONE shi ne:
• Ka duba cikin Xender da kyau, daga can sama (bangaren dama) akwai wasu digo guda uku, icon ≡, sai ka shige shi.
• A menu din, ka duba na karshe, shi ne ‘phone cooy’, sai ka shige shi.
• Sai ka zaba a cikin wayoyin biyu, daya NEW (wacce za a turawa), daya kuma OLD (wacce za ta tura din).