• Leadership Hausa
Wednesday, September 27, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalar Amurka, Kaskar Da Ke Shan Jinin Tattalin Arzikin Duniya

by CMG Hausa
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Dalar Amurka, Kaskar Da Ke Shan Jinin Tattalin Arzikin Duniya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Domin neman dakile matsalar hauhawar farashin kayayyaki a gida, babban bankin kasar Amurka(FED) ya kara ruwan kudin ajiya da kaso 0.75% a kwanan baya, sau uku a jere ke nan da ya kara ruwan da wannan kaso a shekarar da muke ciki.

Sakamakon matsayin dalar Amurka a tsarin harkokin hada-hadar kudi ta duniya, matakin da FED din ya dauka ya sa darajar dalar Amurka ta karu a kan sauran kudade, baya ga kuma farashin kayayyaki ya karu a duniya, matakin da kuma ya juya matsalar hauhawar farashin kaya da take fuskanta a gida zuwa sauran kasashe da shiyyoyi.

  • Kasashen Tsibiran Pacific Ba Za Su Zamo Makamin Amurka Na Aiwatar Da Siyasar Yanki Ba

An ce, tun bayan karuwar darajar dalar Amurka a wannan shekara, darajar kudade 36 a sauran kasashen duniya ta ragu da a kalla kaso 1/10. Misali a nahiyar Afirka, darajar kudin Rand na kasar Afirka ta Kudu ta ragu da kashi 9.4%, yayin da darajar Pound na kasar Masar ta sauka da kashi 18%. A kasar Ghana ma, ko da yake ta riga ta daga ruwan kudin ajiya zuwa kashi 22% don tinkarar matakin kasar Amurka, duk da haka, darajar kudin kasar na ci gaba da raguwa.

A Nijeriya da ta fi karfin tattalin arziki a Afirka, yawan hauhawar farashin kayayyaki ya kai kaso 19.64% a watan Yuli, baya ga kuma adadin ya hau kaso 20.52% a watan Agustan da ya wuce, wanda ya kai wani matsayin kolin tun bayan watan Satumban shekarar 2005.

Abin da kuma ya biyo bayan matsalar hauhawar farashin kayayyaki shi ne dakushewar tattalin arziki, bisa rahoton hasashen tattalin arzikin Afirka na shekarar 2022 da bankin raya Afirka ya fitar a kwanan baya, an yi hasashen bunkasuwar tattalin arzikin Afirka da kaso 4.1% a wannan shekara, wanda ya fado kasa kwatankwacin kaso 6.9% da aka samu a shekarar 2021.

Labarai Masu Nasaba

Ra’ayin Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ta Bai Daya Na Tattaro Karfin Sauya Duniya

Babban Jami’in JKS: Kasar Sin Za Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Amincewa Da Juna Da Kasar Masar

Ta hanyar saka matsalar hauhawar farashin kaya ga sauran kasashe, matsalar da Amurka din take fuskanta a cikin gida ta sassauta, duk da cewa hakan ya faru ne sakamakon hasarorin da sauran kasashe suke biya ta fannonin matsalar hauhawar farashin kaya da tabarbarewar tattalin arziki, lallai abin da mai iya magana kan ce, “Amurka ke ciwo, amma ta sa sauran kasashe su sha magani.”

A hakika dai, tun bayan karshen yakin duniya na biyu, Amurka ta sha yin amfani da kakkarfan matsayin dalar Amurka a duniya wajen kwatan arzikin sauran kasashe da ma saka matsalolinta gare su.

Tamkar dai wata kaskar da ke jinin tattalin arzikin duniya ne, yadda Amurka ke amfani da dalarta wajen kwace dukiyoyin al’ummun sauran kasashe.
Hanya mafi kyau wajen daidaita wannan matsala ita ce, a rungumi manufar kiyaye kasancewar bangarori daban daban, wato kamata ya yi kasa da kasa, musamman ma kasashe masu tasowa su tsaya kan aiwatar da hadin gwiwa a tsakaninsu, wajen kafa wani tsarin hada-hadar kudi mai inganci da ke kunshe da kudade na kasashe daban daban. (Mai Zane:Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare
Previous Post

Amfanin Manhajar XENDER A Wayoyin Hannu

Next Post

“Ka Da Ku Kuskura Ku Zaɓi Masu Kashe Mutane A Zaɓen 2023 — Goodluck Jonathan

Related

Duniya
Daga Birnin Sin

Ra’ayin Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ta Bai Daya Na Tattaro Karfin Sauya Duniya

6 hours ago
JKS
Daga Birnin Sin

Babban Jami’in JKS: Kasar Sin Za Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Amincewa Da Juna Da Kasar Masar

7 hours ago
Kasar Sin Mai Burin Ganin Ci Gaban Kowa
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Mai Burin Ganin Ci Gaban Kowa

8 hours ago
Kimiyya
Daga Birnin Sin

Masana Kimiyya Na Kasashen Kenya Da Sin Sun Kaddamar Da Kundin Farko Game Da Nau’ikan Tsirran Da Kenya Ta Wallafa

9 hours ago
Libya
Daga Birnin Sin

Me Ya Haifar Da Ambaliya A Libya?

10 hours ago
Xi
Daga Birnin Sin

Xi Ya Jaddada Gina Ingantattun Yankunan Cinikayya Maras Shinge Na Gwaji

11 hours ago
Next Post
2023: Cin Fuska Ne Ga Jonathan A Bukaci Ya Sake Yin Takarar Shugaban Kasa —Bulkachuwa

"Ka Da Ku Kuskura Ku Zaɓi Masu Kashe Mutane A Zaɓen 2023 — Goodluck Jonathan

LABARAI MASU NASABA

Hatsaniya Ta Kaure Kan Zargin Cirewa Wata Gawa Ido Daya A Asibitin Kwararru Da Ke Gombe

Hatsaniya Ta Kaure Kan Zargin Cirewa Wata Gawa Ido Daya A Asibitin Kwararru Da Ke Gombe

September 26, 2023
NNPP Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Sauraren Karar Zaben Gwamnan Kano Da Ta Ba Gawuna Nasara

NNPP Ta Kai Korafinta Ga Hukumar NJC Kan Kalaman Daya Da Cikin Alkalan Kotun Zaben Kano

September 26, 2023
Duniya

Ra’ayin Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ta Bai Daya Na Tattaro Karfin Sauya Duniya

September 26, 2023
‘Yansanda Sun Dakile Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Kan Wasu Rukunin Gidaje A Katsina

‘Yansandan Jihar Nasarawa Ta Tabbatar Da Sace Wasu Daliba A Jihar

September 26, 2023
JKS

Babban Jami’in JKS: Kasar Sin Za Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Amincewa Da Juna Da Kasar Masar

September 26, 2023
Kungiyar Kwadago (NLC) Na Shirin Tsunduma Wani Sabon Yajin Aiki Mai Dogon Zango

NLC Da TUC Sun Shirya Tsunduma Yajin Aiki Mai Dogon Zango Ranar Talata 3 Ga Oktoba 2023

September 26, 2023
Kasar Sin Mai Burin Ganin Ci Gaban Kowa

Kasar Sin Mai Burin Ganin Ci Gaban Kowa

September 26, 2023
Da Alamun SAKA Ba Zai Buga Wasa Biyu Ba Saboda Raunin Da Ya Samu Arteta

Da Alamun SAKA Ba Zai Buga Wasa Biyu Ba Saboda Raunin Da Ya Samu Arteta

September 26, 2023
Kimiyya

Masana Kimiyya Na Kasashen Kenya Da Sin Sun Kaddamar Da Kundin Farko Game Da Nau’ikan Tsirran Da Kenya Ta Wallafa

September 26, 2023
Libya

Me Ya Haifar Da Ambaliya A Libya?

September 26, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.