Ko-kun-san….
Sarauniya Amina Nikatau ce ta ki aure domin kar ta rasa karfin ikon fada a ji da na yaki wacce ta mulki masarautar Zazzau bisa jarumta tamkar namiji?
A yau filinmu ya yi ninkaya cikin tarihi tare da zakulo tarihin Sarauniya Amina, mace ce wacce tarihinta ya nunata a matsayin hazika, jaruma ta fuskacin soji da na hidimar rayuwa. Ta kasance mace ce wacce ba ta san tsoro ba, ta ji mulki iya jin mulki, son mulki da karfin iko ne ma ya sanya har ta mace ba ta yi aure ba domin gudun kada aure ya sa ta rasa karfin izzar iko. Ta mulki Masautar Zazzau wacce a yanzu ta dawo Zariya da ke jihar Kaduna bisa kwazo da kokari. Ta kai ga mutuwa ne a shekarar 1610.
Wace Ce Sarauniya Amina Nikatau?
Ta na da kannuwa mai suna Zaria wacce da sunanta ne Turawan mulkin mallaka suka sauya sunan birnin Zariya a farkon karni na ashirin.
A bisa tarihin da wani masaniya Dabid E. Jones ya nakalto, Amina ta tashi ne a karkashin kulawar kakaninta kuma sun fi sonta da nuna mata kauna ta kasance mai amsar umarnin lamuran siyasa da na soja daga garesu.
Ta na da shekara sha shida a duniya aka nadata sarautar Magajiya kana aka ba ta Kuyanga guda 40 da za su mata hidima tukuru. Tun tana ‘yar karamarta, samari da manyan mutane sun yi ta kokarin neman autenta amma ta bijire musu.
Bayan rasuwar iyayenta a wajajen shekara ta 1566, dan uwan Amina ya zama Sarkin Zazzau, a wannan gabar, Amina ta zama jar gwarzo, jaruma, sadauki waccce ta kasance mai jagorantar bataliyar soji a fagen daga. Har ma zuwa yanzu, ana yabonta cikin wakokin Hausa da ake mata kirari da Amina diyar Sarki Nikatau wacce ta samu lambar shaidar jagorantar mazan soji fita fagen daga a matsayin mace mai kamar maza.
Bayan mutuwar dan uwan nata Karami a shekarar 1576, Amina ta dale kan mukamin Sarauniya. Zazzau dai na daga daga cikin muhimman jihohin Hausa wato garuruwan Hausa Bakwai, sauran kuma su ne, Daura, Kano, Gobir, Katsina, Rano da kuma Garun Gabas.
Kafin ma Amina ta hau kujerar Sarauta, Zazzau ta kasance daga daga cikin manyan jihohi. Garin ta kasance asasin samun Bayi da ake saida a kasuwannin Kano, Katsina. A bisa cinikin Bayi, Amina ta sake shimfida mulkinta yadda ta ke wacce ta zama abar mutuntawa da kimantawa daga al’ummar masarautarta da ma yankunan da suke tsoron kar ta dumfaresu da yaki.
Watanni uku bayan hawanta karagar mulki, Amina ta yi gangamin shekara 35 na neman mamaye yankunan da suke daf da Zazzau domin fadada garin daga yankunan makwafta. Sojojinta wadanda suka kunshi sojin kafa 20,0000, sojojin doki 1,000 sun samu horo sosai kuma sun kasance abun tsoro ga abokan gaba wanda ake tsoron su dumfari gari da nufin yaki.
Amina dai ta mace ne ba tare da sanin hakikanin dalilin da jawo mutuwar nata ba. Wani fitaccen malami a karni na sha tara, Dan Tafa ya shaida cewa, “Amina ta mutu ne a wani wajen da ake kira Attaagar”. Dalilin hakan masarautar Zazzau ta fi kowace masauta a fadin yankunan Hausa a wancan lokacin, tun daga jihar Bauchi ta hade da yankuna da dama a shiyyar.
Shi kuma Sidney John Hogben ya bada rahoton cewa, Amina ta mutu ne a Atagara da ke kusa da Idah a yanzu, domin a lokacin Amina ta tura kan iyakokin Zazzau ta Kudu yankin da ke tsakanin jihar Neja da Benuwai. Kan haka dai an yi ta samun rahotonni mabanbanta dangane da mutuwarta da inda ta mutu da dalilin hakan, domin marubuta daban-daban sun yi ta kawo nasu bayanai daban-daban, wasu sun ce ta mutu a Bom Jos, wasu kuma suka ce a Atagara, Idah ta mutu.
A bisa shahararta, wuraren tarihi a nahiyar Afrika da ma wasu yankunan a fadin duniya sun yi ta nakalto bayanai kan tarihinta tare da mannawa cikin kundin tarihin domin ‘yan baya su san wacece Sarauniya Amina wacce ta shimfida mulkin da maza da dama suka kasa yi.
Tarihin baya-bayan nan da aka rawaito kan Amina na nuni da cewa Sarauniya Amina ta kasance mai son yaki da yakar abokan gaba, ba ta tsoron fada ko kadan bisa jarumtarta ne ya sanya ba ta fargabar karawa da abokan fada. Ta samu soyayya da kauna sosai daga wajen Kakarta Marka, matar Kakakanta Sarkin Nohir wanda shi kansa kakanta soyayya ya nuna wa Amina tsantsa.
An bada rahoton cewa Amina ta ki auren kowani da na miji ciki har da sarakunan da suka nemata a zamaninsu ne domin bata son rasa ikon mulki da karfin fada a ji.
Sarauniya Amina ta taimaka wa Zazzau (Zaria) sosai wajen maida ita cibiyar kasuwanci da kafafa yawan fadin kasa. Mahaiyarta Bakwa, ta mutu a lokacin da Amina take da shekara 36 a duniya, inda ta bar mata milkin Zazzau.