Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da babban jakadan Amurka Marco Rubio sun yi gargaɗi a ranar Lahadi cewa za su “bude kofar wutar jahannama” kan Hamas tare da “kammala aiki” a kan Iran.
Jawabin nasu ya zo ne a wata ganawa da manema labarai a birnin Jerusalem, yayin da Rubio ke gudanar da ziyararsa ta farko a Gabas ta tsakiya a matsayin Sakataren harkokin wajen Amurka a gwamnatin Donald Trump.
- Hezbollah Ta Harba Rokoki 165 Zuwa Arewacin Isra’ila – IDF
- Isra’ila Ta Bar Falasɗinawa Sun Fara Komawa Arewacin Gaza
Isra’ila Da Amurka Sun Yi Barazana Ga Hamas
Rubio ya bayyana cewa Hamas dole ne a kawar da ita daga harkokin mulki da na soja, yana mai cewa “ba za a bar su su cigaba da zama rundunar soja ko gwamnati ba”.
A nasa jawabin, Netanyahu ya ce “idan har ba a saki dukkan fursunonin da ke hannun Hamas ba, za mu bude kofar wuta”. Ya ƙara da cewa, da goyon bayan gwamnatin Trump, “ba ni da wata shakka cewa za mu kammala aikinmu kan Iran”.
Shirin Trump Na Gaza
Rubio ya bayyana cewa shirin Trump shi ne kaɗai mafita a yanzu, duk da cewa ƙasashen Larabawa da na duniya suna goyon bayan kafa ƙasar Falasdinu tare da Isra’ila.
A nasa bangaren, Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya ce kafa ƙasar Falasdinu ce kaɗai hanya ta samar da zaman lafiya a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp