A ranar 13 ga watan Mayu, 2025, Gwamnatin Amurka da Saudiyya sun rattaba hannu kan wata babbar yarjejeniyar kasuwanci da ta kai darajar dala biliyan 600.
Shugaban Amurka Donald Trump da Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman ne, suka jagoranci sanya hannu kan wannan yarjejeniya a Riyadh, babban birnin Saudiyya.
- Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe
- Mahaifin Tsohon Gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, Ya Rasu
A cikin wannan yarjejeniya, sama da dala biliyan 140 za a kashe ne wajen ƙarfafa tsaro da sayen makamai.
Ana sa ran hakan zai taimaka wajen yaƙi da ‘yan ta’adda da tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
Sauran fannonin yarjejeniyar sun haɗa da makamashi, albarkatun ƙasa kamar ma’adinai, da kuma fasahar zamani wato Artificial Intelligence (AI).
Masana sun ce wannan mataki zai iya sauya tsarin kasuwanci da ci gaban fasaha a duniya, musamman a yankin Larabawa.
Bayan kammala taron a Saudiyya, ana sa ran zai wuce Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) domin ci gaba da tattaunawa da shugabannin yankin kan batutuwan tsaro da haɗin gwiwar tattalin arziƙi.
Yarjejeniyar ta samu karɓuwa daga ɓangarorin da dama, inda wasu ke ganin hakan zai ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman wajen yaƙi da ta’addanci da bunƙasa fasahar zamani.
Sai dai wasu na nuna damuwa kan yawan makaman da Saudiyya ke saye daga Amurka, suna mai cewa hakan na iya ƙara tsananta rikice-rikice a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp