ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka: Mai Shafawa Sauran Kasashe Bakin Fenti

by CGTN Hausa
2 years ago
Amurka

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony J. Blinken, a gun “taron kolin Demokuradiyya” da aka gudanar a kwanan baya, ya zargi kasar Sin da gurbata yanayin sadarwa, da yada labarai na jabu. Amma ko hakan gaskiya ne? Alal hakika, wane ne ke yada labaran jabu?

Kowa ya san cewa Amurka kasa ce da ta fi yada labarai na jabu da kirkirarsu. Tun lokacin cacar baka, Amurka ta rika sayen kafofin yada labarai karkashin wani shiri mai suna “Operation Mockingbird” don su yi abin da take so.

  • Kungiyoyin Ma’aikatan Jami’o’i SSANU Da NASU Sun Janye Yajin Aikin Gargadi Da Suka Shiga
  • Xi Ya Jaddada Bukatar Kara Amfani Da Filaye Don Bunkasuwar Yankuna Mai Inganci

A shekarun baya-baya nan, ganin yadda Sin ta bunkasa cikin sauri, Amurka ta mai da ita abokiyar takara mafi girma, har ma ta tada yakin bayanai a kanta. Kwanan baya, wani masanin Turai mai suna Jan Oberg ya fayyace cewa, a shekarun baya, majalisar dokokin kasar Amurka ta zartas da wani kudiri na ware kudi har dallar Amurka biliyan 1.5, don horas da‘yan jaridar kasashen yamma cikin tsawon shekaru 5, don su rubuta labaran shafawa kasar Sin bakin fenti. Kaza lika, ba sau daya ba, ‘yan siyasar Amurka ciki har da shugaban hukumar leken asiri ta CIA sun amince cewa, Amurka ta dauki wasu matakai a boye, ciki har da sayen wasu kafofin yada labarai don shafawa kasar Sin bakin fenti, abin da ya shaida cewa, Amurka ta tsai da shirin shafawa Sin bakin fenti cikin dogon lokaci.

ADVERTISEMENT

Yanzu Sin na samun bunkasuwar tattalin arziki mai karko, amma Amurka ta yada labarai wai tattalin arzikin kasar Sin zai dakushe. A yayin da shawarar “ziri daya da hanya daya” ke amfanar al’ummar kasashe daban-daban, Amurka ta ce wai tarkon bashi ne. A yayin da al’ummar kasashe da dama ke bayyana hakikanin abin da suka ji ko gani a Sin, Amurka ta ce wai Sin ta sayi kafafen yada labarai. Ban da wannan kuma, Amurka ta bayyana matakan da Sin take dauka na bunkasa tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al’umma a jihar Xinjiang a matsayin aikin tilas da kisan kare dangi. Shin ko Amurka ta fadi gaskiya? Gwano ba ya jin warin jikinsa.

Hausawa kan ce “Munafuncin dodo ya kan ci mai shi”. Amurka tana yunkurin gurbata gaskiya, amma duk da haka sauran kasashe na fahimtar burinta sosai, kuma ba za a amince da hakan ba ko kadan. (Mai zane da rubutu: MINA)

LABARAI MASU NASABA

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Ta Yaya Za A Iya Tabbatar Da Tsaro A Yammacin Afirka?

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Ta Yaya Za A Iya Tabbatar Da Tsaro A Yammacin Afirka?
Ra'ayi Riga

Ta Yaya Za A Iya Tabbatar Da Tsaro A Yammacin Afirka?

December 17, 2025
Me Ya Sa Aka Kayyade Yin Amfani Da Sinadaran Narkar Da Kankara A Beijing
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa Aka Kayyade Yin Amfani Da Sinadaran Narkar Da Kankara A Beijing

December 16, 2025
Next Post
Tauraron Dan Adam Na Queqiao-2 Ya Shiga Falakinsa A Zagayen Wata

Tauraron Dan Adam Na Queqiao-2 Ya Shiga Falakinsa A Zagayen Wata

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Ceton Dukkan Ɗalibai 230 Da Aka Sace A Neja

Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Ceton Dukkan Ɗalibai 230 Da Aka Sace A Neja

December 22, 2025
Gobara Ta Haddasa Mummunar Asara A Kasuwar Kayan Katako A Kano

Gobara Ta Haddasa Mummunar Asara A Kasuwar Kayan Katako A Kano

December 22, 2025
An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.