Amurka Na Tsoron Korea Ta Arewa Na Iya Kai Mata Hari

Wasu manyan jami’an Amurka guda biyu sun ce akwai yiwuwar Korea ta Arewa ta iya kawo harin makaman Nukiliya akan Amurka nan da wasu ‘yan watanni masu zuwa.

A jiya Alhamis, Darektan hukumar leken asirin kasar ta CIA, Mike Pompeo ya faɗawa a wani taro a nan Washington cewa “yana cikin matukar damuwa” kan yadda Korea ta Arewa ke ƙara zafafa barazanarta da kuma yiwuwarta haifar da gwagwarmayar neman mallakar makaman Nukiliya a tsakanin ƙasashen da ke yankin gabashin Asiya.

“Ya kamata mu riƙa ɗauka tamkar sun cimma wannan buri na su ne,” in ji Pompeo a lokacin da aka tambaye shi kan yiwuwar Pyongyang ta kawo hari akan wasu muhimman wurare a cikin Amurka.

“Tuni sun riga sun yi nisa wajen cimma wannan burin, yanzu an kai wurin tunanin ta yaya za a iya ja musu burki?”

Bayan haka ne kuma, a ranar ta Alhamis, mai ba da shawara kan harkar tsaro Janar H.R McMaster, ya ce hukumomin Washington na faɗi-tashin ganin an shawo kan wannan lamari ba tare da an kai ga ɗaukar matakin soji ba.

 

Exit mobile version