Fadar shugaban ƙasar Amurka, ta sanar da cewa a yau, za a fara amfani da sabon haraji da ya kai kashi 104 a kan wasu kayan da ake shiga da su ƙasar daga ƙasar China.
Wannan haraji zai fi shafar kayan da ake ƙerawa a China kamar na’urorin wutar lantarki, motoci masu amfani da lantarki, kayan fasaha da wasu nau’ukan kayayyakin amfani na yau da kullum.
- Babu Kuɗin Fansar Da Aka Biya Wajen Ceto Janar Tsiga – DHQ
- Kotu Ta Daure Ango Kan Liƙi Da Kuɗi A Wajen Bikinsa A Kano
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ce wannan matakin na ƙara haraji yana da nasaba da yadda China ta lafta haraji mai tsauri kan kayan Amurka da ake shigo da su ƙasarta.
Ya ce idan China ba ta janye harajin nata ba, to shi ma zai ci gaba da ƙara nashi harajin.
Karoline Leavitt, mai magana da yawun fadar White House, ta ce China ta yi kuskure da ta mayar da martani da haraji, kuma ta ce Shugaba Trump zai fi son a samu zaman lafiya da fahimta tsakanin ƙasashen biyu.
Ta kuma ce har yanzu ƙasashe sama da 70 daga sassa daban-daban na duniya sun tuntuɓi Amurka domin a yi tattaunawa kan yadda sabbin harajin ke shafar kasuwanci a duniya.
Mene ne Ma’anar Wannan Haraji?
Wannan haraji na nufin idan ana shiga da kaya daga China zuwa Amurka, za a ƙara musu kuɗi sosai kafin su isa kasuwannin Amurka.
Wannan zai iya sa farashin kayan ya tashi a kasuwa, kuma zai iya janyo taƙaddama a tsakanin Amurka da China, waɗanda su ne manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki a duniya.
Me Ya Sa Wannan Ke Da Muhimmanci?
Wannan rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China na iya shafar farashin kayayyaki a duniya, musamman a ƙasashen da ke dogaro da kayayyakin da ake ƙera su a China ko Amurka.
Sannan zai iya janyo sauyin hanyoyin cinikayya da shigo da kaya, wanda zai shafi kamfanoni da masu siye da kaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp