Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanya ƙasashe bakwai na Afrika a cikin matakin gargadi na “Kada Ku Yi Tafiya” a watan Disamba 2024, bisa ga rahoton binciken tsaro mai zurfi.
Kasashen sun haɗa da Libya, Mali, Somaliya, Sudan ta Kudu, Sudan, Burkina Faso, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR). Gargadin ya nuna barazanar rikice-rikicen da suka haɗa da yaƙi, da ta’addanci, da laifuka, da kuma rikicin cikin gida.
- Ban Ji Dadin Abin Da Libya Ta Yi Wa Super Eagles Ba – Tinubu
- Ban Ji Dadin Abin Da Ya Faru Da Tawagar ‘Super Eagles’ A Libya Ba -Patrice Motsepe
Rahoton ya bayyana cewa a Libya, rikici da ayyukan ta’addanci sun yi muni, yayin da a Mali ake fuskantar garkuwa da mutane da hare-haren ta’addanci, musamman wajen Bamako. Somaliya na fama da laifuka na kisan kai da garkuwa da mutane tare da barazanar hare-haren ta’addanci da fashin jiragen ruwa.
A Sudan da Sudan ta Kudu, rikici da sace-sacen motoci sun yi muni, tare da yawan kashe-kashe a Khartoum tun daga watan Afrilu 2023. A Burkina Faso kuma, ta’addanci da rikici sun janyo dokar ta-baci a wasu sassan ƙasar. A CAR, galibin yankunan ƙasar na ƙarƙashin ikon kungiyoyin yaƙi masu aikata laifuka da garkuwa da mutane.