Kwanan baya, shugaban Amurka Joe Biden ya sa hannu kan dokar ba da izinin tsaron kasa ta (NDAA) ta shekarar kasafin kudi ta 2025. Inda ake yanke shawarar ware kudin ayyukan soja da yawansu ya kai dalar biliyan 895, adadin ya kai matsayin koli a tarihin kasar, matakin da ya bayyana burin Washington a bangaren bukatun karuwar kasafin kudin soja.
Dokar tana yunkurin samun daidaito ta hanyar shafawa kasar Sin bakin fenti har fiye da sau 10, inda ta yi ikirarin cewa wai kasar Sin barazana ce, baya ga haka, ta tsoma baki cikin batun yankin Taiwan, ta kuma ingiza manufar samarwa yankin taimakon makamai, wanda hakan tamkar sako ne maras dacewa ga ’yan awaren yankin Taiwan.
- Mutum 2 Sun Mutu Yayin Da ‘Yansanda Suka Ceto Mutum 10 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Katsina
- Boko Haram Sun Kashe Mutum 2, Sun Jikkata 3 A Borno
Alal hakika, sau da dama Sin ta sha bayyana matsayin da ta dade tana tsayawa a kai game da batun Taiwan, wato “Muradu masu tushe na kasar Sin, kuma abu mafi muhimmanci ga huldar kasashen biyu”.
A watan da ya gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Amurka Joe Biden, yayin da suke ziyarar aiki a Peru, inda suka tattauna tare da cimma matsaya daya kan dabaru 7, da wasu abubuwa masu muhimmanci 4 da dole ne bangarorin biyu su nacewa.
Daga cikin muhimman abubuwan 4, batun Taiwan ne mafi muhimmanci. Kuma yayin ganawar tasu, Biden ya nanata kin amincewa da sabon salon yakin cacar baka, da kin nuna goyon bayan ’yan awaren yankin Taiwan, da dai sauran alkawura na siyasa. Amma, ba da dadewa ba, Amurka ta yi watsi da alkawarinta, ta nuna fuska biyu kan batun yankin Taiwan, matakin zai haifar da rashin tabbaci ga yankin.
Sabuwar gwamnatin Amurka mai jiran gado, za ta fara jan ragamar kasar nan da kwanaki 20 masu zuwa. Dole ne Amurka ta yi taka tsantsan kan batun Taiwan, idan tana son wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da nacewa ga hadaddun sanarwoyi 3 na tsakanin kasashen biyu, da cika alkawarinta da ta yi game da kasar Sin, da bayyana matsayinta a fili, don gane da adawa da ware Taiwan daga babban yankin Sin, da goyon bayan dunkulewar kasar Sin cikin lumana. (Amina Xu)