Wata kotun shari’ar Musulunci da ke Magajin Gari a Jihar Kaduna ta yanke wa wani mutum mai suna Yusuf Usman hukuncin zama a gidan yari na tsawon watanni shida, bayan an kama shi da laifin satar takalman mutane a masallaci.
An yanke hukuncin ne ranar Talata bayan Usman ya amsa cewa ya shiga masallacin ba tare da izini ba kuma ya saci takalma.
- Wani Matashi Ya Ƙone Kansa A Kano Saboda Yana Son Zuwa Aljanna
- An Kama Mutane 26 Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Kogi
Alƙalin kotun, Malam Kabir Muhammad, ya ba shi zaɓin biyan tara ta Naira 5,000 ko kuma ya je gidan yari.
Sai dai ya kuma umarce shi da ya biya Naira 150,000 a matsayin diyya ga kwamitin Masallacin.
Alƙalin ya ƙara da cewa idan Usman ya gaza biyan wannan diyya, zai ƙara shekara guda a gidan yari.
A yayin shari’ar, jami’in ‘yansanda ASP Luka Sadau, ya bayyana cewa wasu daga cikin kwamitin Masallacin ne suka kama Usman a ranar 13 ga watan Yuni, sannan suka kai shi ofishin ‘yansanda.
Ya ce bayan sallar Juma’a, Usman ya sace takalma da kuɗinsu ya kai Naira 100,000.
Usman ya kuma amsa cewa yana yawan zuwa Masallaci a ranakun Juma’a domin satar takalma, sannan ya sayar da su a kasuwannin Monday Market da Maraban Rido.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp