A yau Laraba ne aka bude bikin baje kolin kasuwanci na kasa da kasa wato “Canton Fair” karo na 138 a birnin Guangzhou. Ya zuwa yanzu, bikin ya jawo hankalin sama da masu sayayya dubu 240 daga kasashe da yankuna 218, adadin da ya karu da kaso 10 bisa 100 idan an kwatanta da na bara.
Fadin harabar baje kolin ta kai murabba’in kilomita 1.55, an kuma raba wurin zuwa sassa 55 karkashin manyan sassa 13. A mataki na farko, an kafa wani yanki na musamman na injuna masu ba da hidimi, yayin da a mataki na 3 aka kara wani yanki na musamman na kiwon lafiya ta hanyar fasahar zamani.
Wannan ya nuna sauyin da ake samu a fannin sabon tsarin samar da hajoji, da hidimomi masu karko, da inganci a harkokin kasuwanci na kasa da kasa.
Bikin a wannan karo, ya samar da rumfunan baje koli 74,600, kuma sama da kamfanoni 32,000 sun shiga baje kolin, wadanda dukkansu sun kai sabon matsayi a tarihi. (Amina Xu)