A yau Talata ne aka bude taron dandalin tattauna batutuwan tattalin arziki na Asiya na Boao na shekarar 2023, taron dake gudana duk shekara a birnin Boao na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. Taron na bana na yini 4, ya samu halartar baki kimanin 2000, daga kasashe da yankuna sama da 50.
Yayin taron manema labarai da ya gudana da safiyar yau, mashirya dandalin sun bayyana cewa, taron na bana, ya janyo hankulan jagororin siyasa, da ministoci da tsofaffin manyan jami’ai 92, da shugabannin hukumomin kasa da kasa da na shiyyoyi 11, tare da kuma shugabannin kamfanoni da mashahuran masana da dama.
Taken taron na bana shi ne “Duniya maras tabbas: Hada kai don fuskantar kalubale, bude kofa da yin hakuri don inganta ci gaba”. Kaza lika yayin zaman na safiyar yau, an fitar da rahotanni guda 2, wadanda dukkanin su ke nuni da cewa, daukacin sassan tattalin arzikin nahiyar Asiya za su ci gaba da farfadowa a shekarar nan ta 2023.
Har ila yau, a taron na bana, za a gudanar da kananan dandaloli, da zaman tattaunawa na karawa juna sani, ciki har da mai taken “Ziri daya da hanya daya: Rarraba damammakin bunkasuwa da sabon salon samar da hajojin masana’antu “. (Saminu Alhassan)