An bude taron dandalin tattauna batun tsaro na Xiangshan karo na 12 a yau 18 ga Satumba a cibiyar taro ta duniya ta Beijing, inda ministan tsaro na Sin janar Dong Jun ya halarci taron, kuma ya gabatar da jawabi mai muhimmanci.
Janar Dong Jun ya bayyana cewa, A bana aka cika shekaru 80 da samun nasara a yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun Japan da kuma nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiyya. Ya ce a wannan lokaci mai muhimmanci na tunawa da tarihi da kuma samar da kyakkyawar makoma, ya kamata a rike daidaitattun ra’ayoyin tarihi na Yakin Duniya na Biyu, a tsaya tsayin daka don kare adalci na tarihi, kuma a cimma matsaya daya da fahimtar juna. Ya ce sojojin Sin na fatan kara hada hannu da dukkan bangarori don kare daidaiton ikon mulki, da kiyaye tsarin zaman lafiya bayan yaki, da tallafawa ra’ayoyin kasancewar mabanbantan bangarori a duniya, da kare muradun kasa da kasa na bai daya, tare da inganta tsarin shugabancin duniya. Ya ce ya kamata a bi hanyar da ta dace ta kiyaye zaman lafiya, da bin shawarar ra’ayoyin zaman lafiya, kuma a taka rawar gani wajen tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya, da kuma habaka zumunci cikin lumana, ta yadda za a ba da gudummawa ga zaman lafiya mai dorewa a duniya.
- Shugaban Guinea-Bissau Ya Goyi Bayan Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Da Sin Ta Gabatar
- ’Yan Bindiga Sun Sako Ma’aurata A Katsina Bayan Karɓar N50m A Matsayin Kuɗin Fansa
Wannan taron mai taken “daukaka tsarin duniya da inganta neman ci gaba cikin lumana” ya samu halartar wakilai fiye da 1,800 daga sama da kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa 100, da masana, da masu sa ido daga ko ina a fadin duniya.
Ban da haka, a jiya Laraba, Janar Dong Jun, ya yi kira da a yi dukkan kokarin da ya kamata na karfafa tafiyar da harkokin duniya, da hada hannu wajen gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama.
Dong Jun ya bayyana haka ne yayin taruka daban-daban da ya yi da shugabannin rundunonin tsaro na kasashen Malaysia da Cambodia da Myanmar da Namibia da Rwanda da Senegal, wadanda dukkansu ke birnin Beijing domin halartar taron dandalin tsaro na Xiangshan karo na 12.
Da yake yi musu maraba, Dong Jun ya ce taron na wannan karo na da matukar muhimmanci ga tarihi.
Ya kara da cewa, a shirye rundunar sojin Sin ta ke ta ci gaba da raya dadaddiyar abotar dake tsakaninta da dukkan bangarori wajen karfafa tuntubar juna da hadin gwiwa kan tsaro, da hada hannu wajen tunkarar hadura da kalubale a duniya.
Yayin tarukan, dukkan ministocin tsaron kasa da kasa da suka halarci taron, sun bayyana kudurinsu na karfafa hadin gwiwar soji da kasar Sin.
(Amna Xu/Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp