A jiya ne, aka bude taron kolin kungiyar G77 da kasar Sin a birnin Havana na kasar Cuba.
Taron wanda ya gudana har zuwa yau Asabar, ya tara tawagogi daga kasashe sama da 100.
Li Xi, mamban zaunannen kwamitin hukumar siyasa na kwamitin kolin JKS, kana wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron.
A jawabinsa, Li ya gabatar da wadannan shawarwari, game da hadin gwiwa tsakanin G77 da kasar Sin, na farko tsayawa kan ainihin burin G77 na samun ‘yancin kai, da karfafa hadin gwiwa ta hanyar hadin kai, na biyu bukatar nuna daidaito, adalci da damawa da kowa, na uku neman ci gaba, farfado da hadin gwiwa da samun nasara tare.(Ibrahim)