Daga Ibrahim Muhammad,
Shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa reshen jihar Kano Rabaran Adeyemo Adeolu ya bayyana cewa halin rashin tsaro da ake fama da shi abin bakin ciki ne da damuwa a kasarnan.
Kuma abin da za a yi dan maganin matsalar shi ne haduwar kan al’ummar dan kauda ‘yan’ta’adda tare da tsayawa da dagewa, akan yin addu’a wanda idan ana yi Ubangiji zai ji kukansu ya bada nasarar kauda matsalolin da ake fama dasu.
Rabaran Adeyemo ya ce, wannan matsalar ta rashin tsaro a gaskiya, kamar wata gobara ce da za ta iya cin ko’ina idan kuma ba’a mai da hankali ba wurare da babu wannan irin matsala za a iya wayar gari ya shafe su.
Rabaran Adeyemo ya ce, kar al’ummar jihar Kano su gaji da addu’a a hada hannu kuma da irin kokarin da Gwamnan Kano. Dokta Abdullahi Umar Ganduje yake wajen tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce, a cigaba da addu’a wannan damuwa kar ya shigo jihar Kano a kuma rika yi wa Gwamnatin Kano addu’a na cigaba da samun zaman lafiya a Kano a cikin fahimtar juna da kauna, kar a yarda wani abu na rashin jin.dadi ya shiga tsakani.Ita kuma Gwamnati yakamata ta kara nunka kokarinta wajen tsare rayuka da dukiyoyin jama’a, su kuma jama’a su guji yin kalamai da za su kawo gaba a cikin zamantakewa ayi duk abinda zai kara hada kai da kaunar juna a tsakani.
Rabaran Adeyemo Oluade Samuel ya ja hankalin masu wa’azi a Masallatai da coci akan cigaba da yin kira na zaman lafiya, dukkan wa’azinsu ya zama nasa kaunar juna da zaman lafiya ne idan ana yin haka Allah zai kaunacesu ya mara musu baya karsu zama shugabannin addini da za su rika bakar magana da zai kawo wariya su zama masu hada kan al’umma da koyar da su akan muhimmancin zaman lafiya.