Bisa labarin da Kamfanin Dillancin Labaru na Yonhap na kasar Koriya ta Kudu ya bayar, an ce, shalkwatar kwamandojin Kasar Koriya ta Arewa ta bukaci Koriya ta Kudu da ta nemi gafara game da aikin musanyar wuta da aka yi a tekun Huanghai.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a wannan rana, shalkwatar kwamandojin sojojin Kasar Koriya ta Arewa ta ba da sanarwa, inda aka bayyana cewa sojojin ruwan Koriya ta Kudu sun yi tsokana ga Kasar Koriya ta Arewa a tekun kasar, bayan da jiragen ruwa na sojojin ruwan Kasar Koriya ta Arewa suka tabbatar da kutsen da aka yi a tekun kasar, a kan hanyar komawa kasarsu, sojojin ruwa na kasar Koriya ta Kudu sun fara yin harbi, a sakamakon haka, sojojin ruwa na Koriya ta Arewa suma suka fara mayar da martani.
Shalkwatar kwamandan sojojin Kasar Koriya ta Arewa ta bayyana cewa, dole ne sojojin Kasar Koriya ta Kudu su nemi gafara daga Kasar Koriya ta Arewa, kuma ta dauki alhakin aikata wannan laifi.