Connect with us

LABARAI

An Cafke Basaraken Da A Ke Zargi Da Taimakon Masu Garkuwa Da Mutane

Published

on

Rundunar ‘yan Sanda a jihar Imo ta kama Wani mai sarautar gargajiya a yankin Uba dake garin Awara, karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar Imo. ‘jami’an sun kama mai martaba Eze Andrew Okuegbunuwa bisa zargin sa da hannu wajen kitsa garkuwa da mutane da ake yi a yankin kasarsa da kewaye.

Sauran wadanda su ka shiga komar jami’an tsaron sun hada da wani likitan gargajiya da mutanen da aka samu dumu-dumu a wannan danyen aiki na sace mutane da fashi da makami.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a garin Owerri, wajen gabatar da wadanda aka kama, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Imo, Isaac Akinmoyede ya ce:

“A ranar 28 ga watan Yulin 2020, da misalin karfe 2:00 na rana ne dakarun SARS su ka yi nasarar cafke wani mutumi Eze Andrew Okuegbunuwa mai shekaru 59 da ke garin Awara, karamar hukumar Ohaji/Egbema a jihar Imo, da hannu wajen laifin garkuwa da mutane da sauran laifuffukan fashi da makami.”

“Bincike ya nuna cewa wanda aka kama watau Andrew Okuegbunuwa ya ba masu garkuwa da mutane gudumuwar motar aiki, kirar jif ta samufurin Lexus RX330 mai lamba URM 404 EL.”
Advertisement

labarai