Rundunar ‘yan sanda ta jihar Ogun, ta tabbatar da cafke wasu daliban makarantar sakandaren Comprehensive High School da ke karamar hukumar Ilisan-Remo, Ikenne a cikin jihar kan lakada wa Malaminsu duka.
Kakakin rundunar ‘yansandan jiha, Omolola Odutola ne ya tabbatar da afkuwar lamarin a garin Abeokuta.
Lamarin ya afku ne a ranar Talatar da ta gabata inda gungun daliban su goma, aka zarge su da dukan malamin mai suna Kolawole Shonuga sabida ya kama daya daga cikinsu yana magudin jarrabawa da suke kan zanawa a makarantar.
Hakan ne ya harzika dalibin mai shekaru 18 da sauran tsagerun abokansa dalibai, inda suka yi wa Malamin kwanton bauna akan hanyarsa bayan tashi daga makaranta, suka lakada masa duka.
‘Yan sanda na ofishin gundumar Remo ne, suka kawo wa malamin dauki, inda suka kamo dalibai goma da ake zargi da aikata laifin.
Tuni dai, an gurfanar da su a gaban kotu bisa wannan ta’asar da suka aikata.
Shugaban kungiyar malaman makarantun sakandare reshen jihar (ASUSS), Felix Agbesanwa ya bukaci abi wa malaman hakkinsa kan cin zarafin da daliban suka yi masa, inda kuma ya nuna damuwarsa akan rayuwar malaman jihar.
Agbesanwa ya kuma jaddada cewa, dole ne daliban da ake zargin, su fuskanci hukunci domin hakan ya zama izina ga sauran daliban da za su yi tunanin aikata irin wannan dabbancin a nan gaba.
Gwamnatin jihar ta bakin mai bata shawara ta mussaman kan ilimi, kimiyya da fasaha Farfesa Abayomi Arigbabu ta yi tir da aikata ta’asar da daliban suka yi, inda ta gargadi Iyayen dalibai a jihar da su tabbatar da suna sa ido kan tarbiyar ‘ya’ayansu.